Ƙananan yara miliyan 12 ne ba sa samun wadataccen abinci – Sabo Nanono

0
359

Ministan aikin gona da raya karkara ta tarayya Alhaji Sabo Muhammad Nanono ya ce kimanin kananan yara miliyan 12 ne ke cikin matsalar rashin wadataccen abinci.

Alhaji Sabo Nanono ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai, wanda ya samu wakilcin mai bashi shawara Dr. Adeyinka Onabolu ne ya sanar da hakan a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Alhaji Sabo Nanono ya kara da cewa, tuni gwamnatin tarayya ke ci gaba da yin kokarin samar da wadataccen abinci ga kananan yara a fadin kasa baki daya.

Ya kara da cewa, kananan yara kashi 37 cikin dari ne ke cikin wannan matsala ta rashin girma a sakamakon rashin wadatacce n abinci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here