Ƙarancin guraren binne mutane ya tayar da hankalin jama’ar Kano

0
5116

Masu kula da maƙabartu a jihar Kano sun koka bisa yadda ake fama da ƙarancin wuraren binne mamata a maƙabartun da ke jihar.

Masu aiki a makabartu irin na Abbatuwa, da Gidan Gona sun shaida wa BBC cewa wuraren binne mamata sun yi matuƙar ƙaranci ta yadda a wasu lokutan sai dai su hada gawarwaki biyu a kabari guda saboda cikar da makabartun suka yi.

Wasu daga cikin hanyoyin da ake bi a cikin makabartun na kara tsukewa sannan akwai kaburbura wasu a manne da juna, inda filin da ke tsakaninsu ba shi da yawa, kuma wasun su babu inda mota za ta bi ta shiga cikin makabarta.

Malam Danbaba Muhammad, shugaban ma’aikatan makabartar Abbatuwa, ya ce akwai bukatar gwamnatin jihar ta samar da sabbin makabartu a unguwannin da ke Kano, saboda yanzu a tsakanin kaburbura kadai suke iya binne gawa sakamakon yadda ta cika.

“Hakika muna da matsaloli a makabartunmu; wani lokacin idan mun zo binne mutane muka ga wani(gawa) wanda lafiyar kalau babu abin da ya same shi, sai mu yi kasa da shi mu dora wani a kansa. Wani lokacin kasusuwa za mu tarar, sai mu baje mu sa wani a kai,” in ji shi.

Ya kara da cewa rashin isasshen wurin binne mutanen abin tayar da hankali ne musamman idan aka yi la’akari cewa har yanzu gwamnati ba ta samar da mafita game da matsalar ba.

Ya kara da cewa hakan na faruwa ne saboda gagarumar matsalar rasdhin filin binne mamata.

Haka lamarin yake makabaratar Gidan Gona da ke karamar hukumar Tarauni wadda wani da ke kula da makabartar da bai yarda BBC ta nadi muryarsa ba, ya ce su kan sha wuya kafin su sami inda za a binne gawa sakamakon cikar da makabatar tasu ta yi.

Su ma dai wasu daga cikin makwabtan makabartun sun koka bisa ga yadda gwamnati ta yi burus da makabartun, tare da mika kokon barar samar da karin filayen binne gawa.

Sai dai kwamitin da ke kula da makabartu a Kano ya ce yana da masaniyar halin da makabartun ke ciki, kuma tuni suka gabatar da koken a gaban gwamnati.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here