Ƙarin Farashin man fetur da na lantarki: Ina Muhammad Gudaji Kazaure ya shiga?

0
1314

Sunan Honorabul Muhammad Gudaji Kazaure, ba ɓoyayyen suna ba ne ga al’ummar Najeriya, la’akari da yadda ya shahara wajen tsayawa ya yi magana a zauren majalisar ƙasar nan gaba-gadi ba tare da yin ɗar na yin kuskuren harshen turanci da aka saba magana da shi a majalisar ba.

Haka kuma Muhammad Gudaji Kazaure ya zama tamkar wata muryar talakwan Najeriya wajen amayar da abin da ke ransa na irin halin da al’umma su ke ciki, a zauren majalisar ƙasar nan.

Wasu sun yi imani Gudaji Kazaure na amayar da ra’ayin ‘yan Najeriya da dama ne, domin kuwa abu ne mai wahala majalisar ƙasa ta zauna ba tare da ɗan majalisar ya bayyana irin halin damuwar da talakawan Najeriya ke ciki ba, wanda hakan ne ya sanya ake masa kallon wani gogarma a tsakankanin ƴan majalisar da su ka fito daga yankin arewacin Najeriya.

A cikin watan Yunin shekarar da mu ke ciki sai da Gudaji Kazaure ya bayyanawa duniya ƙudurinsa na neman ganin Shugaba Muhammad Buhari kan matsalar tsaro da ta addabi yankin arewacin Najeriya, la’akari da yadda gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi su ka baiwa cutar Coronavirus muhimmanci fiye da harkar tsaro, wanda shi kuma ya yi imanin kafin cutar korona ta kashe mutum ɗaya a Najeriya, ƴan fashin daji sun kashe mutum 100.

Honorabul Gudaji Kazaure ya ce yana da hujjoji da wasu ƙwararan shawarwari da zai bai wa shugaba Buhari kuma ya yi imani za su yi amfani wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da shi.

Amma adaidai lokacin da Talauci a ƙasar nan ya ke ƙaruwa a tsakankanin talakawan ƙasar nan, domin mutane na tsananin jin jiki. Farashin abinci ya yi tsada, kayan masarufi tsada, tsadar rayuwa, komai tsada. Duk da irin wannan halin matsi da talakawan Najeriya su ka tsinci kansu, amma an wayi gari gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rufe idonta wajen ƙara farashin man fetur da kuma na hasken wutar lantarki.

Ƴan siyasa da ƙungiyoyin fararen hula da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun yi Allah wadai da wannan ƙarin, duba da yadda aka tsinci a halin matsin tattalin arziki, dubbai kuma sun rasa ayyukan yi sakamakon cutar COVID-19.

A wannan gaɓar mafi yawan ƴan Najeriya sun kasa kunnuwansu domin jin muryar Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure akan wannan batu, domin ya kan bayyana ra’ayinsa idan aka samu irin wannan yanayi, amma shiru babu ɗuriyarsa.

Domin ko babu komai jin muryar Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure a kunnuwan mafi yawan al’ummar Najeriya kan haifar da nisahdi tare kuma da samar da wani darasin muhawara a shafukan sada zumunta na zamani.

Abin tambayar ko ina Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure ya shiga?

Abba Muhammad ɗan jarida ne ya rubuto daga Kano. 08032649118 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here