Ƙasar Amurka za ta saye maganin korona da kamfanin Biontech da Pfizer suka samar

0
2399

Gwamanatin Amurka ta sanar da ware dala biliyan biyu domin sayen allurar rigakahin cutar cutar covid-19 har guda milyan 100 da yanzu haka kamfanin Biontech da kuma Pfizer ke kan sarrafawa ta hadin-gwiwa.

Sanarwar da kamfanonin biyu suka fitar, ta ce Amurka za ta karbi allurar rigakafin har guda milyan 100 a matakin farko, sannan kuma kasar za ta sayi karin wasu alluran har guda milyan 500 a nan gaba.

BionTech da ke kasar Jamus da kuma Pfizer da ke Amurka, sun kaddamar da bincike domin samar da allurar rigakahin kariya daga wannan cutar ta covid-19 tun cikin watannin da suka gabata, tare da daukar alkawarin samar da wannan magani a wadace domin sauran kasashen duniya.

Kamfanonin biyu sun ce za a samar da wadannan allurai milyan 100 kafin karshen wannan shekara ta 2020, yayin da za a samar da wasu alluran akalla bilyan daya da milyan 300 kafin karshen 2021.

A farkon wannan wata na yuli ne kamfanin na Pfizer da kuma Biontech suka sanar da sakamakon farko na gwajin da aka yi wa wasu mutane 45 na allurar, sakamakon da ke tabbatar da ingancin allurar, yayin da ake shirin gudanar da wani gwajin a mataki na biyu cikin kasashen Brezil da kuma Argentina nan ba da jimawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here