Ƙasar Saudi Arabia ta janye dokar takaita zirga zirga

0
529

Kasar Saudi Arabia ta sanar da shirin janye dokar takaita zirga zirga da ta sanya a sassan kasar a kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 da kawo yanzu ta kashe mutum dubu 1 da 230.

Sanarwar da ma’aikatar harakokin cikin gida ta fitar ta ce daga yau Lahadi za a janye dokar hatta a biranen Makka da Jidda, inda za a baiwa jama’a damar fitowa don gudanar da harkokin, sai dai sanarwar ta ce har yanzu ba a sa rana dangane da saukar jiragen sama daga wasu kasashen ba, haka zalika babu karin haske kan batun aikin Umara ko Hajji.

Sanarwar ta kuma gindaya sharudda kan janye dokar ciki kuwa har da haramcin haduwar mutane fiye da 50 haka zalika wajibi ne amfani da kallen rufe hanci da baki yayin fita w aje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here