Ƙungiyar ECOWAS ta kasa sasanta rikicin siyasar ƙasar Mali

0
1965

Shugabannin Kasashen Afirka ta Yamma sun kamala taron sun a kwana guda a Mali ba tare da samun nasarar kula yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar kasar ba.

Shugabannin guda biyar da suka hada da na Nijar Mahamadou Issofou dake shugabancin ECOWAS da takwarorin san a Najeriya da Ghana da Cote d’Ivoire da kuma Senegal sun gana da shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Yan adawa a karkashin shugabancin Imam Mahmoud Dicko dake neman ganin ya sauka daga mukamin sa.

Rahotanni sun ce kafin saukar shugabannin a Bamako an samu kwarya kwaryar zanga zangar kusa da tashar jiragen saman kasar daga masu neman ganin shugaban kasar ya bar mukamin sa.

Cikin wadanda suka halarci taron harda Jakadan ECOWAS na musamman tsohon shugaban Najeriya goodluck Jonathan wanda kwamitin sa yayi tayin kafa gwamnatin hadin kai wanda shugaban kasa zai gabatar da kashi 50 na ministoci, yayin da Yan adawa zasu bada kashi 30, sai kuma kungiyoyin kwadago da fararen hula da zasu bada kashi 20.

Kasar Mali ta fada cikin rikicin siyasa tun lokacin da aka yiwa shugaba Ahmadou Toumane Toure juyin mulki, matakin da ya haifar da Yan ta’adda da kuma rikicin kabilancin dake cigaba da rasa dimbi n rayuka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here