Ƴan bindiga daɗi a Kaduna sun kashe wani lauya tare da garkuwa da matarsa

0
3060

Ƴan bindiga sun kashe wani lauya mazaunin Kaduna, Haro Gandu, yayin da suka yi garkuwa da matarsa da kuma yaronsa, a gidansa da ke Tollgate, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Gandu ya kasance ma’aikaci ne a ma’aikatar shari’a, an kashe shi ne bayan da ‘yan bindigan suka afka gidansa a daren ranar Lahadi.

Timothy Gandu, tsohon Kwamishinan tsara tattalin arziki, kuma dan uwan mamacin, ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun shiga gidan ne da karfin tsiya bayan da suka balle daya daga cikin tagogin gidan.

Tsohon kwamishinan ya ce ‘yan bindigar sun fara harbin kaninsa ne a kafada, a lokacin da yayi kokarin guduwa kuma suka harbe shi a baya.

Gandu ya ce bayan da aka kashe shi, ‘yan bindigar suka tafi da matarsa da yaronsa.

Ya ce, “Sun zo gidan ne a daren ranar Lahadi, suka balle taga daya sannan suka shiga gidan.

“Sun fara harbin kafadarsa, sannan suka bishi, suka harbe shi a baya, a nan take ya mutu. Sun yi awon gaba da matarsa da yaronsa.

“Kusan dai labarin ta’addancin da ke faruwa ke nan a ko ina. Yan bindiga na shiga gidaje suna kisa da garkuwa da jama’a.”

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labarin, rundunar ‘yan sanda ta jihar bata ce komai ba akan lamarin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce zai tuntubi D.P.O na ofishin ofishin da lamarin ya faru domin tabbatar da rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here