Ƴan bindiga sun nemi harajin miliyan 7 daga wani gari a Sokoto ko kuma su kai hari

0
3040

Ƴan Bindiga a yankin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sun sakawa mutanen wani kauye da ake kira Laɓau harajin naira miliyan 7 kafin su aminta su ci gaba da zama kauyen nasu.

Tun da farko ƴan bindigar sun kirawo al’ummar wannan ƙauyen ne ta hanyar kiran waya akan lallai su bayar da naira miliyan 7 idan har su na so su cigaba da zama lafiya a ƙauyen na su.

Wannan barazanar ta ƴan bindigar tuni ta sanya al’ummar ƙauyen cikin firgici tare kuma da yin hijira zuwa maƙwaftan ƙauyuka.

Tuni dai al’ummar wannan ƙauye su ka sanar da jami’an tsaron da kuma wakilansu a cikin gwwmnati halin da ake ciki.

Aminu Boza shi ne ɗan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Sabon Birni a majalisar dokokin jihar Sokoto, ya ce mutanensa na cikin wani hali.

“Sun aza musu tara sun ce su kawo naira miliyan 5 ne ko bakwai, kuma ba su biya domin ba su da wannan kuɗin, saboda haka kowanne lokaci su na iya shigowa wannan ƙauye su hakaka su, saboda haka muna kira ga gwamnati da ta yi gaggawar daukar mana mataki”

Aminu Boza ya bayyana cewa har yanzu talakawa ba su gamsu da irin tsaron da sojoji su ke ikirarin su na bayarwa.

A nata ɓangaren gwamnatin jihar Sokoto, ta bakin mai magana da yawunta Muhammad Bello, ta ce tana sane da duk abubuwan da su ke faruwa a yankin. Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya da ta jiha suna yin aiki babu dare babu rana domin ganin sun kawo matsalar tsaro a wannan  yanki.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here