Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata mata mai tsohon ciki a jihar Taraba

0
3434

Ƴan bindiga daɗi sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu da wata mata da talatainin dare a Karamar Hukumar Lau ta Jihar Taraba.

Mai cikin da aka yi awon gaba da ita da misalin 2.30 na dare matar wani dan kasuwa a yankin.

Wata majiya a garin Lau ta shaida wa Aminiya cewa kafin a yi garkuwa da matar sai da ’yan bindigar kusan goma dauke da muggan makamai suka shiga yankin.

Ko a makon da ya gabata an yi garkuwa da mutum bakwai cikinsu har da tsohon dan Majalisar Dattawa a jihar ta Taraba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar DSP David Misal ya ce yana jiran samun rahoto daga ofishin ’yan sandan da ke Lau game da abin da ya f aru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here