Akalla soja 20 ne suka mutu a wani kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa tawagar motocinsu a jihar Borno.
Mayakan kungiyar sun kashe sojojin ne a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, tare da jikkata wasu da dama a harin na ranar Talata, a cewar wata majiyar tsaro.
“An kwashi gawarwakin sojojin da suka mutu zuwa Maiduguri yayin da ake jinyar wadanda suka samu raunuka a wani asibitin soji”.
Majiyar ta ce sojojin na hanayrsu ta zuwa su kora ragowar ‘yan kungiyar ne, amma a hanya mayakan suka yi wa motocinsu lanmbo suka yi ta harbinsu ta kowace kus urwa.