Ƴan Majalisa sun dakatar da shugaba Buhari daga ɗaukar dubban matasa aikin yi

0
3601

Majalisar dattawan ƙasar nan da ta wakilai sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya dakatar da shirinsa na daukar matasan 774,000 aikin gyara a fadin tarayya.

Wannan bukata da yan majalisan suka mikawa Buhari ta biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin kwamitin daukar aiki na majalisar da karamin ministan kwadago da aikinyi, Festus Keyamo.

Tun da farko ƴan majalisan sun kalubalanci Festus Keyamo kan kwamitin mutane 20 da ya kafa don zaben wadanda za’a dauka aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here