29.2 C
Nigeria
Monday, September 27, 2021

Ƴan Najeriya na cikin yunwa ya dace gwamnati ta kawo ɗauki – Yahaya Bello

Must read

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa ƴan Najeriya su na cikin yunwa, kuma ya kamata gwamnati ta kawo ɗauki.

Yahaya Bello ya ce babban dalilin da ya sanya wasu su ka ɗauki matakin fasa rumbunan ajiyar abinci tare da daka wawaso.

Gwamna Bello ya ce duk wanda ke jin yunwa to tabbas a gigice ya ke.

Tun da farko Yahaya Bello ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke hira da gidan talabishin na Channels, in da ya ce ya dace gwamnatin tarayya ta baiwa kowacce jiha a ƙasar nan Naira Biliyan 1, domin hakan zai taimaka wajen tallafawa al’umma.

A cikin makon jiy ne dimbim al’umma a wasu jihohin ƙasar nan suka yi fitar dango suna farfasa duk inda su ke tsammanin an boye kayayyakin abinci da na masarufi suna awon gaba da su, kuma sun shafe ilahirin karshen makon da ya gabata suna cin karensu babu  babbaka.

- Advertisement -spot_img

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest article