Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yace gwamnatinsa ta yi iyaka kokarinta wajen yakar kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar nan da kuma kudu maso kudanci, inda yace ‘yan Najeriya ma sun shaida hakan.
Buhari ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a fadar gwamnatinsa dake Abuja, yayin murnar Sallar layya a wannan Juma’a.
Sai dai shugaba Buhari ya bayyana rashin gamsuwa da halin da sha’anin tsaro ke ciki a yankunan arewa ta tsakiya da kuma arewa maso yammacin Najeriya, inda yace hukumomin tsaron kasar za su iya magance kalubalen da ake fuskanta fiye da kokarin da suke yi a yanzu.
Bayanan na shugaba Buhari na zuwa ne kwana guda bayan harin da ya halaka akalla mutane 5 a cikin garin Maiduguri a jiya Alhamis, wanda ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka harba ababen fashewa kan unguwannin Gwange, Custom da kuma Mairi.
Hakazalika a larabar da ta gabata, mayakan na Boko Haram suka kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum farmaki, yayin da suke kan ziyartar garuruwan Baga da kuma Munguno a ranar laraba, domin rabawa mutane tallafi, sai dai hakar mayakan bata cimma ruwa ba.