Ƴan sanda sun damƙe faston da ya zubar wa ƴar sa cikin sa har sau uku a jihar Ogun.

0
3369

Yan sandan jihar Ogun sun damke wani fasto mai suna Oluwafemi Oyebola mai shekaru 44 da aka kama da laifin yi wa ‘yarsa fyade sannan da zubar da cikin da ya rika yi mata har sau uku.

Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya Sanar da haka wa manema labarai ranar Talata.

Oyeyemi ya ce rundunar ta samu labarin ta’asar da Oyebola ya aikata bayan karar da wata kungiya mai zaman kanta ‘Advocacy For Children And Vulnerable Persons Network’ ta kawo ofishinta dake Owode-Egbado a madadin yarinyar.

Ya ce bincike ya nuna cewa fasto Oyebola dake shugabancin cocin CAC Ogo Oluwa ya fara yi wa yarsa fyade tun a shekaran 2015 a lokacin tana da shekaru 19.

“Fasto Oyebola ya maida ‘yar sa tamkar matar sa tun bayan mahaifiyar ‘yar ta rasu, shi ko mahaifin sai ya maida ‘yar sa madadin uwar, ya rika kwana da ita har yayi mata ciki har sau Uku yana zubarwa.

“Bayan haka fasto Oyebola ya sa yarinyar yin amfani da dabaran bada tazarar haihuwa domin kada ta kara daukan ciki.

Oyeyemi ya ce rundunar ta ce fasto Oyebola na tsare a ofishin su sannan ya tabbatar da duk abinda ‘yar ta fada a Kan sa.

Ya ce rundunar za ta Kai fasto Oyebola kotu da zarar sun kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here