Ƴan sanda sun kama wani tsoho da ya ke ba da hayar ƙaramar yarinya ana lalata da ita

0
3347

Rundunar ‘yan sandan Najeriya shiyyar jihar Taraba ta ce tana gudanar da bincike kan wani tsoho mai shekara sittin da bakwai da kuma ƙarin mutum biyu, bisa zargin killace wata yarinya ‘yar shekara goma sha ɗaya, suka yi mata fyaɗe.

Ana zargin mutanen uku da a halin yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ta ce tana tsare da su, da yin lalata da yarinya tsawon lokaci ta hanyar karɓa-karɓa a Jalingo, babban birnin jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Taraba ya ce tsohon ya riƙa karɓar kuɗi daga wani mutum da kan je a mota ya ɗauki yarinyar ya tafi da ita don aikata lalata.

“Sannan har yanzu akwai wani wanda da alama shi wannan dattijon yana ba da hayanta a wajenshi, wanda kullum da moto yake zuwa ya ɗauke ta, ya kai ta wani wuri, ya je yai lalata da ita,” cewar DSP David Misal.

Ya ce shi ma mai motar tuni suka fara bin sawunsa don kamo shi.

Ɗan sandan ya ce tsohon ne ya fara tsintar wannan ƙaramar yarinya a tashar motar birnin Jalingo, kuma ya ajiye ta a hannunsa tsawon wata uku.

“Yana aikin gadi a wani gidan mai, sai ya shigar da ita, ya yi ta lalata da ita zuwa kusan wata uku da suka gabata. Abin mamaki kuma ba shi kaɗai ya tsaya ba.

David Misal ya ce tsohon ya kuma gayyato abokansa biyu waɗanda suka riƙa zuwa suna yi mata fyaɗe kafin asiri ya tonu.

Ya ce sun duƙufa don kammala bincike da wuri don samun damar gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

‘Yan sanda sun kuma zargi mutanen uku da ɗora wa yarinyar talla da kuma mayar da ita ‘yar aike da rana.

Rundunar ‘yan sandan dai ta ce tuni ta tura ƙaramar yarinya zuwa wani sashenta na musamman don samun kulawar da take buƙata.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here