Ƴan siyasa a ƙasar nan na taka rawa wajen lalata rayuwar matasa – Janar Abdulsalam

0
414

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdusalam Abubakar ya bayyana cewa, ‘yan siyasar kasar nan na tafka babban laifi saboda yadda suke bai wa matasa kwayoyi da makamai musamman a lokutan zabe domin cimma muradunsu a siyasance.

Janar Abdulsalam ya bayyana haka ne a yayin zantawa da manema labarai kan bikin cika shekaru 60 da samu ‘yancin kan Najeriya daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Idan za a iya tunawa dai Janar Abdulsalam shi ne wanda ya jagoranci mika mulki ga farar hula da ake cin gajiyarsa a yau, inda ya mika mulki ga Olusegun Obasanjo bayan ya lashe zaben da aka gudanar karkashin tsarin dimokradiya a shekarar 1999.

Ko da yake tsohon shugaban ya bayyana cewa, Najeriya ta samu ci gaba a cikin tsawon shekaru 60 da karbar ‘yancin cin gashin kanta daga Turawan Birt aniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here