RABA TSAKANIN MASOYA AKWAI TSANANIN CIWO….

0
178

WANI LOKACI a yayin mulkin tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, na ziyarci hedikwatar Hukumar Hisbah da ke unguwar Sharada domin samun bayanai dangane da yadda suke gudanar da ayyukan su. Yana tsaka da shaida min cewa, kotu na aiko musu da hukunci mai sarkakkiya su warware, sai ga sako daga kotun an turo wata dambarwa. Maza biyu sai kuma Mace da Budurwa.

MATAR cikin kuka ta fara da cewa, mijinta ya sake ta da jaririya (na manta Watannin) ya rabu da ita ba ci ba ciyarwa daga ita har jaririyar wacce a lokacin ta zama budurwa. Sannan kuma ba ruwan su da batun ilimi da lafiyar ta. BUDURWA ta samu mijin aure an gama komai sai aka ga dacewar ta gabatar da SAURAYI ga MAHAIFINTA.

MAHAIFI ya kekasa kasa ya ce sam-sam bai gamsu ba ba zai kuma amince SAURAYIN ya auri ‘yar sa ba. Wannan ya sa suka shigar da shi kara gaban kotu, shine da abin ya ci tura aka turo su Hisbah. An tambaye shi dalilin sa na kin auren, ya ce kawai saurayin ne bai yi masa ba. Dalili? Ya ce haka kawai.

SAURAYIN ya sunkuyar da kai kasa ya kasa magana, da kunnen sa yana jin mahaifin budurwar sa yana Ikirarin bai yi masa ba. Kazalika ita ma Budurwar hawaye ne ke fita daga idanuwan ta.

HISBAH sun yi duk yadda za su sulhunta lamarin mahaifi ya ki amincewa. Daga karshe sai suka shiga yi wa Budurwar da Saurayin nasiha. Bayan jan Ayoyin Alkur’ani mai tsarki da Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam dangane da wajabcin bin iyaye.

Budurwar ta zabi rabuwa da Saurayin da ya so zama uban ‘ya’yan ta, ta bi umarnin mahaifinta da bai san yadda aka raine ta zuwa matsayin da ta ke ba.

SAURAYIN ya sha kukan rabuwa da masoyiyar sa don babu yadda zai yi, haka aka rabu Uwa na kuka ‘ya na kuka, amma Mahaifin ko a jikinsa.

Haka na baro Hukumar Hisbah zuciya ta cike da tausayin raba zukatan MASOYA biyu, gami da jinjinawa biyayyar Budurwa ga Mahaifinta. Gami da yabawa sallamawa da mika wuya da Saurayin ya yi.

Leave a Reply