DALILIN DA YASA KUKA GA NA RAME:

2
1643

TARIHINA A TAKAICE:
Assalamu alaikum da farko dai sunana Zainab
Abdullahi, wacce aka fi sani da Zainab
Indomie. Ni cikakkiyar Bahaushiya ce, an
haife ni a Abuja kuma ina zaune a Abuja. Na
yi makarantar Firamare da sakandare a Abuja,
sannan na yi difloma a kan Ilmin Kimiyyar
Kwamfuta a Kaduna.

YADDA NA FARA HARKAR FIM:

Ka san babu yadda Allah ba Ya yi da mutum.

Tun ina karama nake sha’awar kallon fina-
finan Hausa. Ina jin dadi idan ina kallon fina-
finan Hausa. Wannan ne ya ja hankalina, ya
sa na yi burin a rika damawa da ni a harkar. A
haka na tsinci kaina a harkar wanda har
zuwa yanzu na zama wata aba a duniyar
fina-finai.

Kafin na shiga harkar fim na yi fadi-tashi
sosai. Ina cikin fadi-tashin ne Allah Ya hada ni
da Ali Nuhu, bayan na fada wa iyayena sun
amince sai suka damka ni a hannunsa a
matsayin amana. Daga nan ne ya yarda ya
kuma rika sanya ni a cikin fina-finansa. Ba ni
da wani ubangida a harkar fim da ya wuce
Ali Nuhu har yau kuma har gobe. Ya ma wuce
ubangida ya zama uba kuma dan uwana. Fim
din da na fara ko kuma na ce wanda ya
haskaka ni shi ne ‘Garinmu Da Zafi’. Wannan
fim din shi ne fim din da na fi so duk a cikin
fina-finan da na yi.

YADDA NA SAMU LAQABIN INDOMIE:

Na san mutane da yawa za su so jin yadda na
samu lakabin ‘Indomie’ da kuma wurin da na
same shi. Wannan sunan ya samo asali ne tun
ina firamare. Tun a lokacin babu abincin da
na fi so kamar taliya, hakan ne ya sa na
daukaka taliyar Indomie a kan kowane irin
nau’in abinci. Wannan dalilin ne ya sa aka
fara kirana da lakabin ‘Indomie’.

DALILIN DA YASA KUKA GA NA RAME:

A baya idan mutane za su iya tunawa na yi
jiki sosai, a gaskiya idan har kana da jiki to za
ka sha wahala wurin gudanar da sauran
ayyuka musamman ma mu ‘yan fim. Idan
akwai wani rol wanda ya shafi rawa ko gudu
ko tsalle-tsalle, to dole idan har kana so ka
sake, ka ji dadin jikinka sai idan ba ka da kiba,
domin idan kana da kiba bayan an gama za
ka ji ka wahala sosai, sannan ba za ka yi rol
din yadda ake so ba. Don haka ba wai jinya
ko tashin hankali ko tunani ko yunwa ba ne
suka sanya na rame ba, a’a, na rage kiba ne,
wanda ake kira ‘slimming’ da Turanci kenan.

HOTUNAN TSIRAICIN DA KUKE GANI NAWA:

A gaskiya ban san da su ba, mutane ne kawai
suke yi don su bata mini suna. Ana yin hakan
ne don a durkusar da jarumi don a daina yi
da shi. A ce taurarinsa sun dusashe, amma
duk wannan abin da ake yi mini Allah bai sa
taurarina sun dusashe ba. Ana sona kuma
masu kaunata ba su daina ba. Babu abin da
zan ce ga masu yi mini wannan abin sai dai
Allah Ya saka mini. Ka lura duk wanda ya ci
gaba ko ya samu daukaka sai ya fuskanci irin
wadannan abubuwa.

RASHIN FITOWA A FINA-FINAN KWANAN NAN:

Na san mutane za su ce a yanzu an daina yi
da ni, to su sani ba haka ba ne. Idan ba za ka
manta ba a baya na ce maka na yi difloma a
Kaduna, kuma kowa ya sani taura biyu ba za
ta taunu ba. Hakan ya sanya na ajiye harkar
fim har sai da na kammala karatuna, amma
nan ba dadewa ba masoyana za su fara
ganin sababbin fina-finaina.

To kun dai ji abinda tace, ko akwai me sharhi
akai???”

2 COMMENTS

Leave a Reply