An Zabi Sarauniyar Kyawun Arewa

0
519

Aisha Ibrahim ta kasance wadda ta lashe gasar Sarauniyar kyau ta Face of Arewa, na shekara ta 2018, da aka gudanar a jihar Kaduna. Aisha dai ta ce ta shiga gasar sarauniyar arewa, inda kimanin mata19 ne suka nemi gurbin zama zakarar gwajin dafi, na mace mafi kyau a yankin arewa, ta kuma sami nasarar lashe kambin.

Da farko mutanen na tunanin gasar kyau wani abu ne na tir da ake fitar da surar jiki, amma Aisha tace ba haka abun yake ba, ita wannan gasar ba irin wanda ake nuna tsiraici ne ba, babu fitar da tsiraici, ana sa kaya na sutura ne kamar yadda sauran mata ke sawa a gari.

Ta kara da cewa da farko dai ta fuskanci ‘yar matsala na rashin yarda daga wajen iyayenta, amma daga bisani sun aminta da sana’ar daga baya da suka fuskanci, ba kamar sauran gasar sarauniyar kyau ba ne, da ke nuna rashin tarbiya wanda ake fitar da jiki a waje.

Kasancewar ita dalibace, ta bukaci iyaye da su dinga marawa ‘ya’yansu, a duk lokacin da suke yunkurin gudanar da wani abu dake bukatar yi, matukar bai sabawa shariah na addini ko al’adda ba, tare da basu kwarin gwiwa wajen cimma muradansu.

Daga karshe ta ce a wannan zamani ya kamata mace ta fita ta nemi hakkin kanta, matukar ba zata taka ka’idojin adinin ta da al’adarta ba, zama bana mata bane a wannan karni da ake ci ko da mace ta na da aure waji bi ne su nemi na kansu.

Leave a Reply