YADDA AKE WAR -WARE SIHIRI:

0
544

YADDA AKE WAR -WARE SIHIRI

Daga Aliyu Sa’id Gamawa

1) A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai (idan an samu busassu sunfi), sai a nika a zuba cikin ruwan.

2) Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan.

3) Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara).

4) Sai a karanta Suratul A’araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.

5) Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82.

6) Suratul Kafirun kafa daya

7) Falaki da Nasi kafa uku- uku.

8) Sai a karanta wannan addu’a
“Allahumma rabban-nas az’hibil ba’as ashfi wa antash-shafi la shifa’a illa shifa’uk shifa’un la yugadiru sakaman” kafa uku.

9) Sannan za’a iya karawa da wannan addu’a “Bismillahi urkika min kulli shai’in yu’uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika” kafa uku

10) Insha Allahu ta’ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan da sati guda kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi.

Leave a Reply