TUNATARWAR DA MALAM LIMAN YAYI A MAƘABARTA.

0
192

TUNATARWAR DA MALAM LIMAN YAYI A MAƘABARTA…

A yayin da muke tsaye a maƙabarta don gudanar da rufe waɗannan bayin Allah iyayen mu…Gidan talabijin na jaridar NTA sunyi hira da Malam Liman inda acikin hirar yayi wata ƴar gajeruwar tunatarwa kamar haka…

Ya fara ne da faɗin cewa yawan yin surutu acikin maƙabarta a yayin da ake binne gawar mamaci ba daidai bane,da yawan mutanen mu yanzu sun ɗabi’antu da yin surutu da magan ganu marasa amfani acikin maƙabarta,wanda a daidai wannan lokacin babu abinda mamaci yafi buƙata irin addu’a…Amma sai kaji kowa yana magana haya haya,wani ma waya ce za’a kira shi sautin waƙa ya tashi duk yaja hankulan mutane duk da haka bazai kashe ba sai ya ɗauki kiran su cigaba da yin hirar duniya…A gaskiya wannan ba ɗabi’a bace mai kyau,ba’a son yin surutu a maƙabarta matuƙar ba mai amfani bane,misali kamar yima mutum gyara shima ayishi yanda za’a fahimta ba da faɗa ba…

Labarin hirar duniya a lokacin da mutum yake kan hanyar komawa gida bayan rufe mamaci,shima wannan babu kyau domin yin hirar zai sanya ma mutum shagaltuwa da daina tunanin mutuwa a wannan lokacin…

Sannan mayar da wajen zaman gaisuwa wurin cin abinci,hirar siyasa,hirar ƙwallo,gaddama da dai sauransu…Da yawan mutane idan akayi rasuwa shikenen kakarsu ta yanke saƙa domin kuwa da sunga lokacin cin abinci yayi zasu lallaɓo suzo su zauna wasu ma har da abin zubawa suke zuwa suci anan kuma su tafi dashi gida,sunga banza ta faɗi…To a gaskiya shima wannan ɗabi’ar bata kamata da musulmi na ƙwarai ba,domin kai musulmin ƙwarai kaine yakamata ka dafo abincin ka kawo ma iyalan mamatan domin suyi amfani dashi…

Wasu kuma basu da wani aikin yi sai hirar ƙwallo da gaddamar siyasa,wai har sun manta abinda ya tara su a wajen…Duk Musulmi na ƙwarai jajantawa yake zuwa yayi tare da bayar da haƙurin rashin da akayi,yana mai yi musu addu’ar neman gafarar ubangiji…Amma ba zaman hirar duniya ba,shari’a duk bata amince da yin haka ba…

Sannan sai matsala ta gaba afkawa gidan mamaci don yin gaisuwa,malam yace wannan ba daidai bane,domin kuwa bai haltta ba kaje ka cakuɗu da matan da ba muharramanka ba…Amma shikenen baka taɓa shiga gidan mutane ba,kawai yanzu don anyi mutuwa shikenen ka sami tiket na faɗawa gidan mutane,zaifi kyautuwa ka tsaya zaure ka sanya a kira maka wacce kake tunanin ya wajaba akanka kayi mata ta’aziyya…

Ina roƙon Allah ya ƙara ganar damu…Shi kuma Malam Allah ya saka mishi da alkairi,abinda ya faɗi daidai Allah ya bashi lada,wanda kuma yayi kuskure Allah ya yafe mishi…Su kuma iyayen mu Allah ya jiƙan su da gafara…

Leave a Reply