ZA’A DAUKI SABON MATAKIN DA ZAI BAIWA SOJOJIN NIGERIA KARIYA A FAGEN YAKI

0
136

Daga Datti Assalafiy

Maigirma shugaban sojojin Nigeria Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai lokacin da ya shirya taron cin abinci da manema labarai shekaran jiya asabar 22-12-2018 a birnin Maiduguri bayan ya ziyarci dakarun sojoji a fagen daga, yace rundinar sojin Nigeria zata kaddamar da sabon kakin sojoji mai dauke da fasahar zamani ta yanda duk inda sojin Nigeria zai kasance za’a iya ganinshi sannan a kai masa daukin gaggawa idan ya fada tarko.

Shugaban sojojin kara da cewa rundinar sojin Nigeria zata sayo manyan sabbin jiragen yaki marar matuki (drone) masu daukar makami mai linzami (missiles) da zasuci nisan zango wanda za’ayi amfani dasu wajen gudanar da leken asiri da kaddamar da hari a maboyar ‘yan ta’adda.

Yace yin amfani da manyan jiragen yaki marassa matuki abune da zai tallafa sosai a cikin wannan yaki da ake da ‘yan ta’adda, kuma sabon tsari ne na yaki da manyan kasashen duniya suke amfani dashi don haka muma zamu fara amfani da jirgin.

Muna fatan Allah Ya karawa rundinar sojin Nigeria taimako da nasara akan ‘yan ta’adda Amin.

Leave a Reply