Yadda Aka Bankado Ma’aikatan Da Suke Karbar Albashi Sama Da Daya Dubu Hamsim A Nageriya (Ghost Workers) Sanadiyar BVN.

0
249

Basheer Sharfadi

Menene Ghost Workers?
Sune ma’aikacin da yake karbar albashi sama da guda daya. A shekarun baya a Najeriya misali mutum yana aiki a hukumar zabe to sai yaje wata hukumar ya nemi aiki kuma a bashi, baya zuwa amma ana biyansa wannan albashin sai ka samu mutum daya da albashin mutum uku, ya toshe gurinsu.

Idan albashinka na ma’aikatar farko da kake kake aiki ya fito daga TSA Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya zuwa bankin ka sai Remita tayi copy din BVN dinka ta turawa gwamantin tarayya haka in na wata ma’aikatar yazo sai remita ta turawa gwamantin tarayya cewa wane-wane ma’aikaci a hukuma kaza ya karbi albashi sau kaza.

Da aka tsananta bincike sai da aka gano mutane Dubu Hamsin (50,000) masu irin wannan halaryar cikin ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Sai aka dakatar duk wanda aka samu da wannan laifin ya zama albashi daya zai dinga karba, hakan yasa gwamantin tarayya ta samu rara har sama da Naira Biliyan Dari Biyu N200,000,000,000.

Acikin wannan kudinne kwanaki gwamnatin tarayya ta debi ‘yan sanda Dubu Goma (10,000) ake biyansu albashi, ba wai wasu kudin albashinsu ne gwamnatin ta sake fitarwa ba.

To wannan shine yadda aka bankado Ghost Workers.

Leave a Reply