NA FARA BINCIKEN BADAKALAR KWANKWASO – GANDUJE

0
107

Daga Yaseer Kallah

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce yana kan bincikar magabacinsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a kan ayyukan tituna masu tsawon kilomita biyar na biliyoyin naira.

Gwamna Ganduje, wanda ya bayyana hakan yayin da yake kaddamar da kwamitocin kamfen dinsa guda 12 na neman tazarce, ya ce gwamnatin jihar Kano ta mika sha’anin ga hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, EFCC.

Gandujen ya kara da fadin cewa hukumar ta EFCC ta ma yi nisa a cikin binciken yadda aka karkatar da biliyoyin kudin da aka ware domin gina tituna masu tsawon kilomita biyar a kananan hukumomi 44 na jihar zuwa kamfen din kujerar shugaban kasar da Kwankwaso ya yi a shekarar 2015.

Ya ce ya zuwa yanzu, hukumar ta EFCC ta gano yadda aka karbo kudaden daga kananan hukumomi 44 da kuma yadda aka canja su zuwa dala.

Leave a Reply