WASIKAR MUTANEN BORNO GA BUHARI:

1
399

A Bai Wa ‘Yan Sanda Bindigar Kakkabo Jirgi

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

A ranar Litinin ne wasu manyan wakilan jihar Borno suka kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda suka damka masa wata wasika mai dauke jerin wasu abubuwa guda 12 da suka lura da su a kan matsalar da jihar take ciki, da kuma bukatu guda 10. Tawagar wakilan, wadda ta kunshi tsofaffin gwamnoni guda biyu, shuwagabannin gargajiya, dattijai, ‘yan majalisar dokoki na tarayya da jiha, shuwagabannin kananan hukumomi, wakilan kungiyoyin mata, kwadago da ‘yan jarida, shugaban Jama’atu Nasril Islam da shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya, ta samu jagorancin gwamnan jihar, Kashim Shettima.

Gwamna Shettima, wanda ya zubar da hawaye yayin da yake gabatar da jawabi, ya damka wa shugaban kasa wasikar me dauke da wasu manya-manyan abubuwan da suka lura da su guda 12, da kuma bukatu guda 10 da suke so shugaban kasa ya taimaka masu da su.

Duk da dai tawagar wakilan jihar ba ta bayyana bukatunsu ga idon duniya ba, wata majiya mai tushe ta bayyana cewa wasikar ta rabu bangare biyu. Bangare na farko na dauke da abubuwa guda sha biyun da suka gano, dayan bangaren kuma na dauke da bukatu guda goma da suke so a yi wa al’ummar Borno. An harhada dukkan bayanan yayin wani taron tattaunawa ta musamman kan tsaro da gwamnan ya hada, wanda ya samu halartar manyan jami’an soji, da sauran jami’an tsaro. An gabatar da tattaunawar ran Litinin, 31 ga watan Disamba, 2019, a birnin Maiduguri.

Daya daga cikin hasashen ya bayyana wa shugaban kasa cewa rundunar ‘yan sandan jihar Borno, wadda ke dauke da alhakin kare rayuka da dukiyar al’umma, na fuskantar matsalolin karancin jami’ai da kuma dogaro ga bindigar AK-47 gurin fuskantar mayakan Boko Haram din da ke amfani da kirar AA (bindigar da ke kakkaboji jirgi). Hakan ya sanya suka roki shugaban kasa da ya duba yuwuwar damka wa rundunar ‘yan sandan jihar Bornon bindigar AA domin su sami karfin gwiwar tunkarar ‘yan ta’addan.

Bayan wannan sai kuma tanbaya game da me ya sanya ba a tura mafi yawan ‘yan kato da goran jihar, Civilian JTF, wadanda hukumar sojojin Nijeriya ta dauka aiki jihar Borno ba, duk kuwa da cewar tsofaffin ‘yan kato da goran sun fi rashin tsoro da kuma sanin ainahin garin.

Bugu da kari, wasikar ta bayyana wa shugaban kasa cewa sama da ‘yan kato da gora 26,000 da ke taimaka wa sojoji gurin yaki da Boko Haram na amfani da kananan makamai. Hakan ya sa wakilan suke so shugaban kasa ya yi duba ga yuwuwar hada kai da majalisar dokoki gurin damka wa wasu ‘yan kadan, kuma zababbu daga cikin ‘yan kato goran makaman da doka ta amince a yi aiki da su na dan wani lokaci kuma karkashin umarnin soji.

Majiyar ta kuna bayyana cewa wasikar ta sanar wa da shugaban kasa cewa wasu daga cikin ‘yan kato da goran, wadanda suka yi nisa a cikin aikin harhada bayanan sirri tare da tantancewa da damke mayakan Boko Haram din da ke labe a cikin al’umma, na matukar damuwa a kan aikin da ake na maido da ‘yan Boko Haram din da suka tuba cikin al’umma. A cewarsu, hakan zai iya haifar da samuwar ‘yan leken asirin ‘yan ta’adda.

1 COMMENT

  1. Comment:mutan borno said Ku dau hakuri kuyi ta addua Allah ya kawo sabuwar go mnati wadda za ta saurare Ku ta saurari kukan Ku amin

Leave a Reply