Baturiyar Ingila da ta musulunta ta kafa kungiyar mata musulmi na Nijeriya (FOMWAN) a 1985

0
184

Ko kun san cewa da littafan da ta rubuta ne ake koyar da addini a makarantun Sakadire a Nijeriya
(Islamic Studies for senior secondary school)

Ko Wace ce Aisha Lemu?

An haifi marigayiya Bridget Aisha a garin Poole na yankin Dorset na kasar Ingila a 1940.

Tana da shekara 13 da haihuwa sai ta fara tunanin sauya addininta, inda ta fara da duba addinan Hindu da na Bhudda amma basu gamsar da ita ba.

Ta yi karatun jami’a a makarantar koyon al’adu da harsunan kasar Sin da na Afirka a jam’iar Landan (SOAS), inda ta karanta tarihi da al’adu da kuma harshen kasar Sin.

A jami’ar ne kuma ta fara haduwa da dalibai Musulmai wadanda suka rika ba ta litattafan addinin Musulunci, kuma ba da daewa ba sai ta musulunta a shekarar 1961, a lokacin tana shekararta ta farko a jami’a.

A lokacin ne ta bayar da gudunmawarta wajen kafa kungiyar dalibai Musulmai na makarantar ta SOAS a jami’ar Landan, kuma ita ce sakatariyar kungiyar ta farko.

Bayan ta kammala karatun digiri na farko a jami’ar Landan, sai Aisha Lemu ta koma domin karatun babban digiri a kan harshen Ingilishi, kuma a lokacin ne ta fara ganin Sheikh Ahmed Lemu, wanda shi kuma ya isa Landan ne domin karo ilimi a jam’iar ta Landan.

Bayan kammala digirinta na biyu sai ta koma Kano a 1966, inda ta fara koyarwa a makarantar nazarin Larabci, a lokacin shi Sheikh Ahmed Lemu ke shugabancin makarantar. a nanne ta shaku da shi ta suka fara maganar aure har Allah ya tabbatar ya Aureta

An daura mata aure da Ahmed Lemu a watan Afrilun 1968, inda Aisha ta kasance matarsa ta biyu.

Bayan auren su sai kai tsaye ta nemi izinin sa Domin cigaban ayyukan ta ta tafi Sokoto domin kama aiki a matsayin shugabar makarantar mata ta gwamnati.

Daga baya ta koma jihar Neja bayan da aka kirkiri jihar daga cikin jihar Arewa maso yamma ta da a 1976, kuma ta zama shugabar makarantar horar da malamai mata ta Minna har 1978.

Ita da maigidanta sun kafa Gidauniyar Ilimin Islama (IET),ita dai kuma ta kafa babbar kungiyar mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) a 1985.

Ta wallafa littafai da dama a fannin addinin Musulunci da ilimi wadanda aka rika amfani da su a makarantun sakandare na Najeriya, wanda a cikinsu

The Role of Women and Marriage
The Ideal Muslim Wife and Husband
Animals in Islam
Book: The Young Muslim
Islamic studies for senior secondary schools
Woman in Islam

Aisha Lemu ta rasu a ranar Asabar din da ta gabata tana da shekaru 79 a duniya bayan dan gajeruwar rashin lafiya a garin Minna babban birnin jihar Neja.
Allah ya jikan ta da rahama yasa Aljannan fiddausi ce makomar ta,

Leave a Reply