Yan Adawa Kake Yaka Ba Cin Hanci Da Rashawa Ba – Atiku ya caccaki Buhari a kan batun Ganduje

0
250

Daga Yaseer Kallah

Dan takarar kujerar shugaban kasar Nijeriya karkashin tutar jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan matakin da ya dauka game da zargin karbar rashawar da ake yi wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Yayin da yake jawabi a gun wani babban taron tattaunawa mai taken “‘Yan Takara”, da gidauniyar MacAthur, tare da hadin gwiwar gidan talabijin din NTA da DARIA Media suka shirya a Abuja, ranar Laraba, shugaban kasar ya ce ya yanke shawarar ba zai yi komai ba game da batun Gandujen saboda majalisar dokokin jihar ne ke da ikon daukar mataki.

Sai dai a wani jawabi da Paul Ibe ya fitar jiya a madadin Atikun, ya zargi Shugaba Buharin da yunkurin kare kansa daga laifin kin daukar mataki a kan badakalar amsar rashawar da ake zargin Gwamna Ganduje da aikatawa.

Ya ce sam bai gamsu da uzurin da shugaban kasar ya bada ba saboda be nuna irin wannan turjiyar ba a lokutan da yake Allah-wadai da zargin cin hanci da rashawar da ake wa wasu daban da ba ‘yan jam’iyarsa ta APC ba.

Ya ce Buhari ya yi maganganu na rashin adalci a lokuta da dama game da takaddamomin wadanda ba ‘yan jam’iyar APC ba har ma yake zamowa tamkar al’kali ta hanyar hukunta su da kalamansa a gida Nijeriya da ma kasashen waje.

“Wannan nuna bambancin da shugaban kasa yake ya fi komai takaici, kuma shi ne ke tabbatar da cewa yakar ‘yan adawa yake ba cin hanci da rashawa ba,” in ji Atiku.

Bayan nan Atikun ya soki shugaban kasa a kan kare Babachir Lawan, korarren sakataren gwamnatin tarayya, SGF.

Ya ce karin lalacewar ma shi ne yadda shugaban kasa ya kare daya daga cikin ‘yan gaban goshinsa, Babachir Lawan, wanda ya ce ba za a iya tuhumarsa ba saboda rashin hujjoji.

Leave a Reply