ANYIWA KAKAKIN RUNDUNAR YANSANDAN JIHAR KANO SP MAJIA CANJIN WAJEN AIKI ZUWA JIHAR YOBE.

0
523

Mukaddashin babban sufetan yansandan kasar nan, Muhammadu Abubakar Adam shine ya bada umarnin sauya masa wajen aikin kamar yadda takardar sanarwar ta nuna tun fitarta a daren ranar Talata 22-01-2019

Canjin wajen aikin da akaiwa SP Majia baizo mana da mamaki ba duba da haka dama aikin d’amarar ya gada yau kana wannan gari gobe kana wancan gari, babu wani dalili na fili da ya nuna haka face wannan.

Dole kanawa suyi hakuri da wannan sauyi da aka samu na hazikin dansanda wanda yai shura wajen tsayawa akan gaskiya da yin abinda ya kamata na tafiyar da aikinsa tsakani da Allah a iya tsawon shekarun da ya dauka yana wannan mukami.

Tabbas sauyin hakan babu dadi ba haka muka soba amma dole muyi hakuri, sabo akewa kuka ba komai ba.
👇
SP Majia ya zama dansanda abin ayi koyi da shi domin yana yin bakin kokarinsa akan aikinsa ba sani babu sabo wajen ganin anyiwa kowa adalci da yin aiki ba dare ba rana duk domin Al’ummar Jihar Kano.

SP Majia yayi fafutuka sosai wajen ganin an dakile harkar yandaba da bangar siyasa da su kansu yan siyasa domin Jihar Kano ta zauna lafiya ba tare da fargabar wani rikicin siyasa kona kabilanci ba.

Yayi kokari sosai bakin yadda zai iya ba za’a ce dari bisa dari ba domin shima dan Adam ne kamar kowa zai iya yin dai dai ko kuskure amma Alhamdulillah ya kwatanta yin dai dai fiye da kuskure.

Abubuwan fada na alkairi wanda SP Majia yayi domin ingantuwar aikin dansanda a Jihar Kano da kasa baki daya suna da tarin yawan gaske da bazasu lissafu ba kuma Alhamdulillah yaga ribar hakan, Jama’a kuma sun gani.

SP Majia a iya tsawon lokacin da ya dauka yana aiki a Kano ya samu lambobin yabo dana girmamawa daga mabanbantan mutane da kungiyoyi daga ciki da wajen kasar nan.

Dole a wannan ga6ar mu kara godewa Allah da Al’ummar Jihar Kano bisa hadin kai da aka bawa kakakin rundunar yansandan Jihar Kano, SP Majia wajen tabbatuwar tsaro da samun zaman lafiya a birni da kawaye na Jihar baki daya, tabbas SP Majia shine yake bin Al’ummar jihar bashi.

Muna addu’ar Allah ya sakawa Majia da mafificin alkairin duniya da lahira, ya Allah ka zama gatansa, ka rubanya alkairanka gareshi, ka kawo masa babban rabo.

Ya Allah ka bashi ikon cigaba da aikinsa bisa gaskiya da jajircewa a sabon wajen aikin da ya samu kanshi, ka bashi kariya akan makiyansa da mahassadansa a duk inda suke.
Ameen

Ibrahim Rabiu Kurnaa
23-01-2019

Leave a Reply