Fardusoshi Sun Daina Sakani A Film Shiyasa Nadawo Siyar Da Kunun Aya, Inji Chiroki.

0
599

A wata hira da gidan talbijin na Arewa 24 ya yi da shi, Chiroki ya yi ikirarin cewa fardusoshi da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a cikin fini-finai, lamarin da ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya.

Wani Mai amfani da shafin Twitter mai suna Doctor Kiyawa, ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi, amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai

“A Kannywood ne za ka ga mace ta shigo film wannan shekarar amma ta fi wanda ya yi shekara 10 yana sana’ar film kudi.

Ali Nuhu, kai ne wanda yanzu jama’a suke gani da kima a Kannywood, don Allah ku yi wa [Chiroki] wani abu wanda shi ma ba zai manta da kun yi masa halacci ba.”

Sai dai a jerin sakonnin martanin da Ali Nuhu ya mayar wa masu irin wannan korafi, ya kalubalance su da su nuna masa irin taimakon da Chiroki ya bai wa Kannywood.

“Zan yi maka tambaya: lokacin da Chiroki yake tashe wa yataba taimaka wa? Maimakon haka, a kan kudi mene ne ba ya yi wa fardusoshi? Ya kamata mu san abin da muke yi.

Ya ce bai kamata a rika yi wa ‘yan Kannywood rashin adalci ba wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu. Jarumin ya ce babu wani da ke Kannywood da zai taimaka wa Chiroki, yana mai cewa ya kamata ya dawo masana’antar ya sasanta da fardusoshi sannan ya ci gaba da aiki kawai.

Leave a Reply