Ku daina amfani da sunan NNPC domin cimma muradinku na siyasa – NNPC ga ‘yan siyasa!

0
195

Kamfanin man fetur na kasa NNPC ya gargadi ‘yan siyasa musamman masu neman kujerun mulki da su guji amfani da sunansa ko na manyan ma’aikatanta domin cimma burinsu na siyasa.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta bakin kakakinsa, Ndu Ughamdu a jiya, ya ne da ‘yan siyasan da su sani cewa NNPC kamfani ne gwamnati da bai da bangare a siyasa kuma ke aiki da gogaggu da suka san aikinsu tare da rashin nuna banbanci a siyasa, kabila ko addini.

Sanarwar ta kara da bayyana cewa, duba da matsayinsa na babban hanyar samar da kudi ga kasa bai kamata a na alakanta shi da siyasa ba.

Kamfanin ya bukaci ‘yan siyasa da ke amfani da sunansa a siyasance da su sani cewa ba a kafashi da domin sauraron irin haka ba. Kuma ya bayyana cewa ba zai ci gaba da lamunta ba.

Leave a Reply