ZUWAN SHUGABA BUHARI ZAMFARA, ZAI YI SANADIYAR TADA ZAUNE, JAMI’AN TSARO SAI AN YI SHIRI MAI KYAU! In Allah ya nufa, ranar

0
460

Daga Abdulmalik Sa’idu Gusau

In Allah ya nufa, ranar lahadi 3-2-2019, shugaba Muhammadu Buhari, zai shigo jahar Zamfara. Domin yakin neman zabensa Karo na biyu, a matsayin Shugaban kasarmu Nijeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari, ina ganin in ka debe Sardauna da Tafawa Balewa, ba a taba ‘yan Adam mai farin jini kamarsa ba. Mu dai tallaka Muna matukar kaunarsa, Wanda ya sa duk Wanda ya daga mu ke ganinsa fes!

Hakan ya sa ‘yan siyasa masu Hali kusa da shi da ma wadanda su ka yi hannun riga da shi su ke rikonsa domin dafawa. Sheda ce abunda ya faru a 2015 Inda da dama daga cikin bata garin ‘yan siyasa suka shiga rigarsa guguwar Buhari ta Kai su ga madafun iko. Hakan ya sa kowane Dan siyasa a 2019 ya rike habar rigar yana son tumaya ya shiga. Wasu ba ba a jam’iyar APC din su ke ba, Amma suna rika rigar Shugaban dan ya isar da su…..

Sai dai in gizon ke Saka a jahar Zamfara shi ne; har yanzu ba mu da tabbacin ‘yan takarar da za su yi takara a jam’iyar APC da Shugaban ke Jagoranta. Don haka ‘yan takarkari Tara daga jam’iyar APC da dukkaninsu ke takarar Gwamna, kowane na kan bakansa na Marawa Shugaban baya. Kuma na tabbatar ranar da Shugaban zai zo, dukkaninsu za su fito magoya bayansu tare da tambarin wadanda suka goyawa baya. Domin nuna goyon baya ga Shugaban.

Abun tsoro a nan ranar da Malam Ibrahim Wakkala (Mataimakin Gwamnan Zamfara ) ya sawo tikitin tsayawa takara, mun ga yadda aka sanya ‘yan ta’adda suka lahanta wasu magoya bayansa, haka ranar da tawagar magoya Bayan ‘yan takara 7 suka shigo Gusau, an samu hatsaniya. Ranar da Marafa ya zo Gusau, har filin jirgi aka isko mutane aka sassare su. Wannan kenan.

Idan muka dubi yadda aka samu rasa rayukka a lokacin zaben fitar da gwani na jam’iyar, duk da cewa kowa yana da a Gundumar da ya ke jefa kuri’a, ne. To ina ga yanzu da za a hadu a dandamali daya?

Dan haka Muna amfani da wannan damar mu yi Kira dukkanin bangarorin jami’an tsaro na kasar nan. Da su dauki matakin tsaro na musamman, domin kaucewa hasarar rayukka da dukiyoyin al’umma a lokacin da Shugaban zai shigo jahar Zamfara. Domin mu talakawan jahar ne, abun zai shafa, domin an hore mu da jahilci da rashin aikin yi tunanenmu ya karanta, kullum sai hada mu da kayan Maye ake yi tare da ba mu makamai Muna yakar junanmu.

Allah ya sa wannan koken ya Kai ga wadanda mu ka yi shi domin su, tare da share Muna hawayenmu.

Allah ka ka Muna shugaba Buhari lafiya, ka maida shi lafiya, ka tsare Muna shi, ka cigaba da ba shi karfin guiwar yi Muna adalci.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

30-1-2019

Leave a Reply