DAYA BAYAN DAYA SUNA GIRBAN MUMMUNAN SAKAMAKON ABINDA SUKA DASA A ZUCIYAR JAHILAN MABIYANSU

0
468

Daga Datti Assalafiy

Wannan hoto da kuke gani hoton Mamman Nur Alqadi ne, yayi karatun addinin musulunci sosai, Malami ne, tare da dashi Muhammad Yusuf ya fara da’awar Boko Haram tun a farkon shekarar 2000

Mamman Nur sai da ya zama na biyu a matsayi cikin kungiyar Boko Haram.
Mamman Nur asalinsa ‘dan kabilar Shuwa-Arab ne wandanda suka fito daga wani kauye da ake kira Marowa a arewacin ‘kasar Kamaru, a lokacin da Mamman Nur suka fara yada akidar ta’addanci tare da Muhammad Yusuf Abubakar Shekau ba’a ma san da shi ba, daga baya ne Mamman Nur ya gabatar da Shekau ga Muhammad Yusuf

Bayan haduwar Shekau da Muhammad Yusuf sai ya zamto cewa Muhammad Yusuf ya jawo Abubakar Shekau jikinsa saboda kabilanci, har ya zamto cewa Shekau ya karbe matsayin Mamman Nur wato matsayi na biyu a cikin da’awar ta’addancin kungiyar Boko Haram, shi kuma Mamman Nur ya dawo matsayi na uku

Kamar yadda nace Mamman Nur yayi karatun addini sosai domin yafi Abubakar Shekau karatu da ilmi nesa ba kusa ba, amma Shekau yafi Mamman Nur kwarewa a yaki, shi Mamman Nur sam ba mayaki bane, aikinsa kawai karantarwa da canza tunani zuwa akidar ta’addanci, don haka sune masu matukar hatsari

A shekarar 2009 lokacin da Muhammad Yusuf ya shelanta jihadi suka dauki makami har aka hallaka Muhammad Yusuf, sojoji sun samu nasaran harbin Abubakar Shekau a kafarsa, kuma a lokacin an gano Abubakar Shekau inda aka boyeshi a wani gida a cikin garin Maiduguri ana masa jinyar harbin bindiga, amma umarni yazo daga gurin maciya amanar Nigeria cewa kada a kama Shekau, anan aka sulale da Shekau zuwa cikin birnin Kano, suka nemi hayar wani gida katangace ta raba gidan da gidan tsohon shugaban ‘yan sanda na ‘kasa IGP Hafiz Ringim (rtd) sukaci gaba da masa jinya

A cikin wannan gidan ne Mamman Nur yace a kafa sabuwar kungiya mai suna Jama’atu Ansarul Muslimina fiy buladis-Sudan, wanda tafi shahara da (ANSARU) zaiyi mubayi’ah, kuma Shekau suka fara shugabantarwa kafin Abu Mus’ab Khalid Al-barnawiy, da sukaga Intelligence zasu ganosu a wannan gidan shine sai suka fitar dashi zuwa Potiskum, zuwa Bama, kafin ya shiga jejin Sambisa tare da Mamman Nur a karshen shekarar 2012

A farkon shekarar 2014 lokacin kungiyar Boko Haram basuyi mubayi’ah ga kungiyar ISIS na duniya ba, watarana ‘yan Boko Haram sun shirya harin da zasu kaddamar a garin Mubi na jihar Adamawa, sai Mamman Nur yace zaije yakin, akace masa kai ba mayaki bane kayi zamanka a sansani kaci gaba da karantarwa, sai yace shi dai a kyaleshi zaije ya gwada

Bayan da aka kyaleshi suka tafi kaddamar da hari a Mubi, suna tsakiyar harin, kuma sun fatattaki sojoji da sauran jami’an tsaro a lokacin, sai ga wani jirgin yakin Nigeria ya kawo agajin gaggawa wa sojojin da suke ‘kasa, jirgin yana ta jefa bom akan tawagar ‘yan Boko Haram, sauran mayakan Boko Haram da suka kware a yaki duk suka kwanta a ‘kasa, shi kuma Mamman Nur yana kan babur baida dabara na yadda zai kaucewa illar bom

bayan jirgin yakin ya jefa wani katon bom, bomb idan ya fashe yana sakin iska mai matukar karfin gaske wanda yana iya tsinka jikin mutum yayi gunduwa gunduwa, iskar da take tare da bomb wanda jirgin yakin Nigeria ya jefa ta kai ga Mamman Nur dake kan babur sai tayi jifa dashi ya fadi a tsakiyar kwalta, anan ne ya samu mummunan rauni a kafadarsa ma barin hagu, tun daga lokacin kafadarsa bai sake yin aiki ba

Lokacin da Boko Haram zata rabe gida biyu saboda sabanin da ya kunno a tsakaninsu, Shekau yana ta hallaka manyan kwamandojinsa saboda tsoron juyin mulki, ya dinga kitsa makirci yana kashe kwamandojinsa irinsu Mustapha Chadi, Kaka Allai Malam Ali, Baa Gwamna, Baba Abdulmalik, Abu Mujahid, Malam Tahir, Abu Amr Fallujah da sauransu

Anan ne su Mamman Nur da Habib Muhammad Yusuf Al-barnawiy sukayi karar Shekau ga ISIS, sai suka nemi yin mubayi’ah, sai ISIS tace kowanne bangare su rubuta wasika su fadi gaskiyar abinda yake faruwa, a cikin wasikar da su Mamman Nur suka rubuta sai suka fadi dukkan kashe-kashen mutanensu da Shekau yakeyi saboda tsoron juyin mulki, da yadda yake wuce ka’ida a cikin ayyukansu na ta’addanci, a karshe ISIS ta shugabantar da su Mamman Nur suka dawo karkashin ISWAP tayi watsi da Shekau

Wannan abin yayiwa Shekau zafi a ranshi, bai sake cin nasaran yaki ba tun daga lokacin, haka manyan kwamandojinsa suka dinga guduwa zuwa bangaren su Mamman Nur, Shekau yana ta neman hanyar da zai hallaka Mamman Nur shine sai ya nemo wasu amintattunsa “Jasus” wato masu “leken asiri” wanda a turance ake kira da “spy”, suka tafi gurinsu Mamman Nur, kuma sun samu nasaran hallakashi a kwanakin baya, yau an wayi gari wallahi jama’a Mamman Nur baya raye

Wannan shine yadda akayi aka hallaka Mamman Nur ba kamar yadda wasu masu sharhi akan tsaro suke cewa wai Al-barnawi ne ya kashe shi saboda karya ka’ida da yayi akan sakin matan Dapchi da suka kama a jihar Yobe

Kisan Mamman Nur babban asarace a cikin da’awar Boko Haram da dukkan wata da’awa na ta’addanci a wannan nahiya tamu ta afirka, ba ‘dan ta’adda ko mai harin kunar bakin wake (suicide bomber) bane matsalar, suwaye Malamai masu cusa akidun ta’addanci cikin zukata itace babbar matsalar, to abinda Mamman Nur ya kware a kai kenan wajen cusa akidun ta’addanci ga jahilan mabiyansu

Shekau ma yana dab da girban sakamakon abinda ya jima yana aikatawa na ta’addanci insha Allah.
Allah Ka rusa kungiyar Boko Haram, Ka kara jefa sabani da rabuwar kai a tsakaninsu duk su hallaka junansu Amin

Leave a Reply