Sheikh Albani Zaria: Tunawa Da Babban Masoyin Muhammadu Buhari

1
567

Daga Yaseer Kallah

A lokacin da ake tunkarar babban zaben 2011, shahararren malamin addinin Musulincin nan na garin Zaria mai suna Sheik Awwal Adam Albani ya sadaukar da lokuta da dama na wa’azinshi gurin gaya wa mutanen da ke da damar yin zabe abin da za su yi tsammani idan Buhari ya samu nasara. Ya gargadi ‘yan Nijeriya kan kada su yi tsammanin wata mu’ujiza idan Janar din ya samu nasara, saboda a yanayin da zai tarar da kasar, ba wani abu da zai iya aiwatarwa a shekaru hudun farko sama da dakatar da lahanin da ake yi wa kasar.

Sheik Albani ya kara da fadin cewa Buhari zai tarad da kasar a cikin muwayacin halin rashawa da almubazzarancin da dukkan yunkurin da zai yi gurin yin wani abu sabanin su ba zai haifar da da mai ido ba, saboda zai shagaltu gurin gusar da kazantar da ya tarar.

1 COMMENT

Leave a Reply