Wasu ‘yan bindiga sun bude wa wasu motoci wuta a jihar Zamfara.

0
401

Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a kan direbobi a titin da ya bi ta karamar hukumar Zurmi zuwa Gurbin Baure duk ajihar Zamfara.

Tuni dai dire daya ya mutu inda ‘yan bindigar su ka yi awun gaba damutanen dake cikin motocin da har yanzu babu bayanai kan adadinsu.

Al’uman yankin da abin ya faru sun bayyana cewa sun fara jin karan harbin bindiga ne da kusan karfe 3 na ranan jiya Asabar. Su ka ce kafin jami’an tsaro su isa inda abin ya faru ‘yan bindigar sun gudu.

Aukuwan lamarin ya kawo kwan-gama ga al’uman mazauna yakin da lamarin ya faru, saidai jami’an tsaro sun nemi hadin kan a’uman tate dabasu tabbacin kariya ga lafiyarsu.

Leave a Reply