BAMBANCIN SHEKARAU DA SAURAN ‘YAN SIYASA!

0
297

Daga Bello Muhammad Sharada

Shekarau yana cikin mutum 30 da hukumar zabe INEC ta kasa ta sahalewa ya tsaya takarar sanata a Kano ta tsakiya. Yana takara ne a jam’iyyar APC mai alamar tsintsiya.

Mallam Ibrahim Shekarau yana da bambanci da sauran masu takara, a fuskoki guda bakwai.

Shekarau malamin makaranta ne. A tarihin siyasar Najeriya, masu kwarewa a fanni biyar ne suke kan gaba. Malaman makaranta sune farko, domin da Sardaunan Sakkwato da Tafawa Balewa da Aminu Kano da Shehu Shagari duk malaman makaranta ne. Sai lauyoyi su Awolowo, sai ‘yan jarida da marubuta su Nnamdi Azikwe, sai masu damara irinsu MD Yusuf, sannan ma’aikatan gwamnati ‘yan admin. Kano Central ta yi sanatoci guda biyar, cikinsu babu malamin makaranta. Duk masu neman wannan kujera a yau a duk jam’iyyun babu malamin makarantar da ya kai Shekarau. In akwai a fada mini.

Fuska ta biyu, Shekarau tsohon ma’aikacin gwamnati ne, wanda ya kure wa aikin maleji. Ya san ciki da bayan aikin gwamnati, babu a inda za a layance masa. Cikin masu neman wannan kujera babu wanda ya taka wannan matsayin. Abin sha’awa Shekarau ya zauna da kantoman soja da gwamnonin farar hula amma, ya gama aiki ba a taba tuhumarsa da kowacce irin almundahana. A masu neman babu mai wannan shaidar.

Abu na uku, Shekarau ya yi gwamnan Kano shekara takwas a jere. Duk jinsin mutanen Kano babu wanda ya yi kuka da shi. A lokacin da ya yi gwamna kudi tsaba na mutanen jihar Kano naira biliyan 582 suka biyo ta hannunsa, aka yi amfani da su don al’umma amma bai dauki sisin kwabo ba ta haramtacciyar hanya. Cikin masu neman wannan kujera babu wanda ya taba yi gwamna. Mutum daya ne cikinsu ya rike kananan hukumomi 15, dayan kuma a inda yake warkajaminsa a karamar hukuma ce kwaya daya jallin jal. Babu hadi a tsakanin wanda ya yi gwamnan Kano Ta Dabo, Jallabar Hausa da sauran.

Na hudu, Shekarau ya taba zama zababben dan takarar shugaban kasa na jam’iyya ta kasa a shekarar 2011. A zaben ya samu kuri’a dubu 900. Wannan yana nuna ko ina a fadin Najeriya, Shekarau yana da jama’a. Wannan matsayin da ya kai ne aka yi shirin gidan talabijin na BBC HardTalk da shi, sannan ya shiga muhawar ‘yan takarar shugaban kasa da gidan talabijin na NN24 suka shirya har ya zama zakara. A cikin wadanda suke neman wakilcin mutanen Kano Central babu wanda ya taka wannan matakin. KO AKWAI? Ku ce mini babu.

Da Shekarau aka yankewa jam’iyyar APC cibiya, kuma da shi aka yanka mata ragon suna. APC ita ce jam’iyya ta ‘yan hamayya ta farko a tarihin Najeriya da ta kafa mulki. Ya san kowa a cikinta, kowa kuma ya san shi. Da ya shiga jam’iyyar PDP tare da shi da Sanata Ike Ekweremadu suka yi aikin yi wa PDP gyaran fuska da saita ta bisa turba. A lokacin da yana gwamna shi ne kadai gwamnan da bai yi canjin sheka ba ya tsaya daram a jam’iyyarsa ta ANPP. Duk masu takarar Sanata Kano Central babu mai wannan gogewar.

Ya yi.ministan ilimin tarayyar Najeriya na tsawon wata goma. Ma’aikatar ilimi ita tafi kowacce ma’aikata girma da fadi da kwaramnniya. Shi ne.mutum.na farko wanda ba Farfesa da ya rike ma’aikatar a tarihi kuma ya yi abin kirki. Ku fada a cikin masu neman wannan kujerar sanata, wa ya yi ko da ministan sati ne? BABU KAWAI

In kun cire suk abubuwan nan guda shida, ina son ku gaya min mai shiga sabgar jama’a a cikin maneman kujerar, ina nufin yaje daurin aure da janaza da ta’aziyya da duba maras lafiya. Akwai limami cikinsu?
Wane a cikinsu ke daukar waya da amsa tes, ya saurari tsoho da tsohuwa da yaro. Waye mai tausayi da jinkai da hakuri da yafiya, cikakken dan dimokuradiyya? Waye cikinsu zaka ao neman naira dari ya baka 200?

Zaka iya gaya masa kowanne suna Duna, Kamaye, Wakilin Arna, Yaci kudin Makamai, Dan ci da addini ko.Mayaudari koMatsoraci, IYAKARTA KENAN

AMMA Wadannan abubuwan shi ne bambancin Shekarau da sauran. Me wannan gogewar da banbamcin shi ya kamata mu aika wakilci a majalisar dattawan Najeriya

TALLA NAKE YI: KUMA BAN YI KARYA BA

Leave a Reply