‘YAN SIYASA BA SA KASHE KANSU AKAN SIYASA SAUYA SHEKA SUKE YI…

0
226

Akwai rayuwa bayan zabe. Kar ka bari harkar siyasa ta hada ka rigima da wani. Kayi siyasa mai tsafta cikin mutunci da girmama juna. Ka girmama ra’ayin wanin ka shima ya girmama naka.

Ta’addanci da bangar siyasa bata dace da duk mutum mai hankali ba, kar ka bari wani dan siyasa yayi amfani da kai wajen tayar da tarzoma a cikin al’umma. Kar kayi zaton ‘yan siyasa suna amfani da kai ne don ci gaban kasar ka, suna amfani da kai ne su mulke ka don jin dadin rayuwar su.

Ka sani ‘yan siyasa ba sa kashe kansu akan siyasa sauya sheka suke yi zuwa wata Jam’iyyar.

Leave a Reply