Ba Ruwan APC Da Kafa Katafariyar Tsintsiyar Abuja – APC

0
285

Daga Yaseer Kallah

Kafa katuwar tsintsiyar, wacce take alama ta jam’iyar APC, ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya, inda wasu ke tambayar me ya sanya za a kafa alamar wata jam’iya a guri mai matukar mahimmanci kamar babbar kofar shiga Birnin Tarayya (FCT).

Sai dai a wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin din Channels, sakataren yada labaran jam’iyar APC, Mallam Lanre Isa-Onilu, ya bayyana cewa ‘yan Nijeriyan da ke goyon bayan gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne suka kafa katuwar tsintsiyar.

Da yake mayar da martani ga Allah-wadai din da PDP ta yi a kan tsintsiyar, kakakin jam’iyar APCn ya ce wa ‘yan hamayyar su ma su kafa nasu alamar.

Leave a Reply