BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SANATA DR. RABIU MUSA KWANKWASO

1
1414

Daga Datti Assalafiy

Cikin bakin ciki da takaici na yanke shawaran rubuta maka wannan budaddiyar wasika domin soyayyar da nake maka a matsayinka na mutum mai kishin arewa biyo bayan kalmominka da na saurara wanda ka fitar akan wasu Malamai sai ka kauce ka soki Sunnar Annabi Muhammad (SAW)

Maigirma Sanata idan mukace zargin da ka yiwa wasu Malamai gaba dayansa karya ne hakika ba mu maka adalci ba, na tabbata kana da naka shaida da dalilai da yasa ka bayyana mummunan dabi’ar wasu Malamai, amma daga karshe sai ka dabawa cikinka wuka ta hanyar cin zarafin sahihiyar Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW) saboda fusatar da kai da wasu Malamai sukayi

A cikin maganganun da Kwankwaso yayi a matsayin raddi ga wasu Malamai yace ya san Malaman da sukaje suka musuluntar da ‘yan matan inyamurai, daga bisani sai sukebi ‘yan matan suke nemesu da lalata, sannan yasan wasu Malamai da suke zuwa garinsa su karbi kudi da sunan addini sai su cinye lokacin yana Gwamnan Kano

Kwankwaso yace babu ruwansa da wai don Malami yana barin gemu idan har ya tabashi to zaici mutuncinsa ya dura masa ashariya ko yasa yaranshi suci mutuncin Malamin, ya kara da cewa ba wai Malami yana daga wando ba ko bente Malami yake sakawa yake yawo dashi sai yaci mutuncinsa.
Wadanda suka cikin WhatsApp group dina guda 3 na daura muryan Kwankwaso da yake wadannan maganganu aje a saurara

Da farko: Ba zanyi inkarin wasu kalmomi kai tsaye da Kwankwaso ya furta a kan wasu Malamai ba, tabbas cikin wasu kalmomi da ya fadi akan wasu Malaman gaskiya ne, wasu Malaman barnar da suke tabkawa a cikin al’ummar musulmi da cin amana wallahi ko jahili ba zai iya aikatawa ba, ga fitinar neman mata kamar ayu, da auri saki, wannan abune da kosan kowa ya sani babu wani boye boye

Abu na biyu: Kwankwaso ya tafka babban kuskure da barna inda ya fito karara yaci mutuncin Sunnar Annabi (SAW) wato sunnar ajiye gemu da dage wando, sabanin dake tsakanin Kwankwaso da wasu Malamai bai kamata ace ya fusata har ya kauce daga kan hanya ya fada sukar Sunnah ta Ma’aikI (SAW) ba, don haka ina kira ga Kwankwaso ya tuba ga Allah, saboda ba ma masa fatan Allah Ya kwashe masa albarka a dalilin ya soki Sunnah

Abu na uku; Na ga wasu bayin Allah har sun fara tsinewa Kwankwaso albarka suna kafirtashi, laifinsa bai kai ga kafirci ba, kuma bai cancani a la’anceshi ba, a bashi uzuri na jahiltar addini da Sunnah, a samu Malamai amintattu su je su masa nasiha shi yafi dacewa

Abu na hudu: Mu tuna alherin Kwankwaso, Kwankwaso ‘dan kishin arewa ne, a cikin manyan ‘yan siyasar da muke dasu a arewa rayayyu kadan ne irinsa masu kishin arewa, ku tuna lokacin da aka kama ‘yan arewa a Lagos aka musu sharri cewa ‘yan Boko Haram ne, Kwankwaso ne yaje ya dauka musu lauyoyi aka kubutar dasu, mu tuna lokacin da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi yaci mutuncin ‘yan arewa ya kashe wasu ya kama wasu yasa aka musu sharri cewa ‘yan Boko Haram ne, Kwankwaso ne ya dauki lauyoyi aka kubutar dasu

Mu tuna lokacin da aka kashe ‘yan arewa a Ile-Ife Kwankwaso kafin gari ya waye ya isa garin domin yabi kadin ‘yan arewa, nawa muke dasu a cikin ‘yan siyasa masu kishi irinsa? wallahi basu da yawa, kazafi da sharri da batanci mafi muni da za’a yiwa ‘dan arewa shine a alakantashi da kungiyar Boko Haram wacce take kungiya mafi hatsari a cikin jerengiyar kungiyoyin ta’addanci na duniya, idan an maka sharri kai ‘dan Boko Haram ne kowa sai yaji tsoronka, amma Kwankwaso yake zuwa ya kubutar da ‘yan uwanmu da ake musu sharri da kasancewa ‘yan Boko Haram saboda kishinsa ga ‘yan arewa

Inda ace Kwankwaso ya tsaya tsakaninsa da Malamai tunda bai ambaci suna ba wallahi ni dai ba zan fito nace zan kare wani Malamin da ban gamsu da shi ba balle har na masa budaddiyar wasika ko raddi, mu nuna bakin ciki sannan mu nausar dashi saboda ya taba Sunnah, amma bai dace ba muci mutuncinsa saboda ya soki wasu Malaman da ba mu san su waye ba

Muna rokon Allah Ya sa Kwankwaso ya fahimci kuskurensa ya tuba ya kuma gyara Amin

1 COMMENT

Leave a Reply