KO DA BUHARI KO BA SHI ZAN CI ZABE – GANDUJE

0
1499

A wata hirar awa biyu da aka yi da Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi a gidajen rediyon jihar. Ganduje yayi bayani akan masoyan Buhari irinsu Danbilki Kwamanda da ke cewa a zabi Buhari kada a zabe shi.

“Wannan wa ya ke ta shi shashasha mai baki da kunu, ban da cin mutuncin mutane ba abinda suka iya”

Amma sun ce da Buhari bai daga hannun ka ba za ka samu matsala?

“Wannan kujerar da nake kai Buhari bai daga hannuna ba, kuma zabe na ba tare da na Buhari za a yi ba ballanata ace zai taimaka min. Mutanen jihar Kano shaida ne ko da Buhari ko ba shi in Allah Ya yarda za mu ci zabe. Muna yin Buhari saboda jajircewar sa, kuma ba wanda zai hana mu tallansa.”

Majiya Sarauniya.

Leave a Reply