Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci ‘yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Omar, wacce Musulma ce ‘yar asalin kasar Somaliya, da ta yi murabus bayan da ta wallafa wasu sakonni a shafinta na Twitter.

0
290

Sakonnin da ta wallafa dai na zargin cewa ‘yan majalisar dokokin Amurkan na goyon bayan Isra’ila ne kawai saboda kamun kafa da kudi.

Shugaba Trump ya bayyana cewa ”ko dai ta yi murabus a matsayinta na ‘yar majalisa ko kuma ta fita daga kwamitin majalisar a kan harkokin kasashen waje.”

‘Yar majalisar mai wakiltar jihar Minnesota ita ce ‘yar Somaliya ta farko da aka fara zaba a majalisar.

Misis Omar dai ta ba da hakuri bayan ta sha suka daga mutane daban-daban a kan wannan lamari.

‘Yan jam’iyyar Democrat da kuma Republican a kasar sun bayyana cewa sakonnin da ta aika a shafin Twitter ya jawo ce-ce-ku-cen kan batun kin jinin Yahudawa.

Shugaba Trump ya bayyana kalaman da Misis Omar ta yi na ba da hakuri a matsayin kalamai marasa gamsarwa.

Leave a Reply