Babbar Magana Buba Galadima Ya Hango Ranar Mutuwar Buhari

0
4828

Buhari bashi da koshin lafiya, duk wanda ya zabi Buhari, to Osinbajo ya zaba – Buba Galadima Ma’ana Buhari Zai Mutu Bayan Zabe Kenan..
Mun samu labari cewa Buba Galadima, wanda yana cikin masu magana a madadin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar yayi magana game da batutuwan da su ka shafi zaben da za ayi kwanan nan.

Injiniya Buba Galadima yayi wata hira wadda ta shigo hannun majiyarmu inda ya bayyana cewa duk wanda ya zabi shugaba Muhammadu Buhari, ya san cewa mataimakin sa watau Yemi Osinbajo kurum ya sakawa kuri’a ba kowa ba.

Galadima wanda a da yake tare da Buhari ya dai karyata cewa ya juyawa gwamnatin APC baya ne don an hana shi kujerar Minista. Dattijon yana ganin cewa idan ma za a duba sakayya, ya cancanci shugaba Buhari ya ba shi wani mukami.

Dattijon yace Buhari bai cika alkawuran da ya dauka a baya ba domin harkar tsaro ta sake tabarbarewa a mafi yawan jihohin kasar nan, sannan kuma tattalin arziki ya rushe. Galadima yace tun daga taron Kano, APC ta san cewa ta fadi zabe.

Alhaji Galadima kuma ya karyata surutun da ake yi na cewa Diyar sa tana aiki a Aso Villa, yace idan har da gaske ne a fadi mukamin ta.

Galadima yace shi Buhari da kan sa ne ya bada auren Diyar nan ta sa kuma tana da Digiri har 5.

Tsohon Sakataren na jam’iyyar CPC wanda ta narke cikin APC ya kuma bayyana cewa babu wani aikin a zo a gani da Buhari ya tabuka musamman a Arewacin Najeriya don haka ya nemi a zabi Atiku Abubakar domin ya gyara kasa.

Leave a Reply