DA DUMI- DUMI: EFCC TA KAMA BABBAN MAI DAUKAR NAUYIN TAKARAR ATIKU…

1
5437

Daga Ibrahim Hamza

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta cafke wani babban mai kula da kudaden da ake kashewa a takarar dan takarar shugaban kasa na jam’yyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, mai suna Uyi Giwa-Osagie.

Majiyar Mu, ta ruwaito wata majiya ta karkashin kasa ta bayyana cewa EFCC ta kama Uyi ne a ranar Litinin, 18 ga watan Feburairu, amma ta sakeshi bayan ta gudanar da bincike akansa tare da yi masa wasu yan tambayoyi na tsaown sa’o’i 9 a ofishinta.

Shi dai Uyi babban lauya ne, kuma shine babban mai kula da duk kudin da ake kashewa a takarar Atiku Abubakar, wanda ya hada har da yakin neman zabe, don haka yana daya daga cikin amintattu, na hannun dama kuma na kusa da Atiku.

“Atiku baya kashe kudi a takararsa kai tsaye, Uyi Giwa ne ke kashe duk kudin da ake bukata a yakin neman zaben Atiku, ta hannunsa Atiku yake antaya kudi cikin yakin neman zabensa.

“Don haka kamashi da EFCC tayi ka iya haifar da takarar Atiku, musamman game da zirga zirgan wakilan zabe da zasu kare mana kuri’unmu a kowanne rumfa da kuma biyansu kudadensu.” Inji wani kusa a kwamitin yakin neman zaben Atiku.

Allah ya kyauta ameeen

© Ibrahim Hamza

1 COMMENT

Leave a Reply