Komishinan zabe a jihar Adamawa ya karyata zargin karban cin hanci daga Atiku

0
308

Babban jami’in hukumar zabe mai zamnan kanta a jihar Adamawa, Alhaji Kashim Gaidam ya karyata jita-jita da ke yawo na cewa dan takaran shugabana kasa, Atiku Abubakar na jam’iyar PDP ya bashi cin hanci domin magudin zabe har Dala Miliyan Daya.

Komishinam ya bayyana hakan ne a yau Litinin a Birnin Yola, fadar jihar, inda ya bayyana cewa, zai iya ratsuwa ba tare da kaffara ba, bai taba ganawa da Atiku ba, sannan ya ce ta ya ma dan siyasan zai fara bashi wannan kudi har da gida da ake cewa a kasar Dubai bacin basu taba haduwa da sunan ganawa ba? Ya karyata wannan rade radi tare da cewa wasu baragurbin ‘yan siyasa ne kawai da ke naman suna ke kokarin haddasa wannan fitina.

Gaidam ya ce shi ba irin mutanen da ake sayan mutunci da darajarsu bane da kudi.

Leave a Reply