ME YA HANAKA TONAWA KWANKWASO DA SURUKINSA ASIRI?

0
215

Daga Datti Assalafiy

Sanannen ‘dan jarida Jaafar Jaafar wanda ya fitar da video na zargi akan Maigirma Khadimul Islam Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya wallafa wannan rubutun a shafinsa na racebook tun ranar 25-9-2018 kamar yadda za’a gani a wannan screenshot.

Idan ba wata boyayya a kasa Malam Jaafar a matsayinka na ‘dan jarida da kariyar da kake takama da shi na dokar aikin jarida ya kamata ka tona asirin Kwankwaso da na Surukinsa amma sai kace wai an hanaka, waye ya hanaka?

Indai wadanda suka sa ka saki videon batanci na zargi akan Maigirma Gwamnan Kano domin su cimma burinsu na siyasa, to bai kamata ka boye wani abu da ka sani akan abokan adawarsa ba a matsayinka na ‘dan jarida, wannan shine adalci.

Ina kuke mutanen Kano? ya kamata ku tilasta wannan ‘dan jarida ya fada muku boyayyen abu game da Kwankwaso da Surukukinsa kar kuje kuyi zaben da zaku dawo kuna da na sani, domin babu shakka akwai wani mummunan abu a kasa da yake boye a kansu kuma ‘dan jaridar ya sani amma yace wai an hanashi yin rubutu a kai.

Malam Jaafar Jaafar lokaci yayi da zaka ceto al’ummar jihar Kano daga fadawa hannun su Kwankwaso da surukinsa, idan kayi haka duniya zata yarda kai ‘dan jarida ne na gaskiya wanda ba wasu kake yiwa aiki ba.

Allah Ya kyauta.

Leave a Reply