Babu shakka Hadiza gabon ta Tirsasa Amina Amal ne ta fadi abunda ta fada, bada son ranta ba.

0
2067

 

A wani Video da dazu wani Producer ya turo min, inda Hadiza Gabon take wulakanta wannan yarinya Amina Amal, a cikin Video Hadiza gabon take dukan yarinyar nan tana tursasa ta akan ta karanta wani rubutu dake cikin wayar ta, (Text) data turo mata, har marinta ta takeyi, tamkar yarta.

Kafin inyi magana akan wannan Bidiyo yaka mata mu koma baya, a Bidiyon farko.

A cikin Video Farko akwai inda Hadiza Gabon take fadawa yarinya cewar, “Rannan da kika zo gidana kike ce min idan kina saduwa da namiji bake kawo wa sai Kin tunani”.

Wannan maganar yaka mata ace mu dauke ta muyi mata kaca-kaca saboda akwai abubuwan tambaya a ciki, yaka mata mu fyedeta, yanda ya kamata.

Shin farko meya kawo wannan maganar?

Zancen gaskiya idan babu wani abu tsakanin Hadiza Gabon da Amina Amal, babu yanda za’ayi irin wannan hira ta batsa ta shiga cikin su tun farko ma tukun, domin wannan babbar magana ce kuma sirri ne, sai in halin ku daya kuna fadawa juna, iskancin ku da kukeyi.

Sannan magana ta biyu itace kalmar “Sai na tunaki” tambaya anan shine dame zata tuna da hadiza gabon? Shin idan babu wani abu zaiyu a tuna da wani abu kuwa? Dole ya kasan ce akwai wani abu da sun kasan ce sunayi a tsakanin su, Amma da Amina amal ta tona asiri kuma sai Hadiza Gabon tana so tayi duk mai yuwa wajen wanke kanta, daga zargin da amal tayi mata. Duk da cewa, “gaskiya ne ba zargi ba bane, Gabon kokari take taci mutuncin yarinyar ta hanyar duka da tsoratar wa, domin ta wanke ta da bakin ta, amma zancen gaskiya Gabon ba wankakkiya bace. Ta iskan tar da yarinya, da abu ya isheta ta fito duniya ta tona asiri, sai ta nemi wulakantata, saboda taga bata da kowa anan kasar.

Sannan dangane da maganganun Video na farko, ba duka Bane zai iya zama gaskiya abunda ya faru bane, domin an tursasa mata ne ta fadi abunda ta fada, wato cusa mata maganganun da zatayi akayi bada son ranta ba.

Wani Producer dazu da safe ya turo min da magana ta murya ta manhajar WhatsApp Amma bazan ambaci sunan sa ba, yana cewa, ai maganar yarinyar a Video dakuwa tayi, an saka mata magana ne shiyasa ta fadi abunda ta fada, amma yace min zancen gaskiya maganar hakan take babu wani zargi, har yake cewa, “In tambayi kaina mana Shin bayan Film me hadiza gabon takeyi ne? Sanna yace min kaso 99 na matan film yan Iska ne har yayi ikirarin yan Mad’dugo ne, wannan maganar ta fito daga cikin Wanda ake damawa dashi kenan a harkar.

Wato idan maganar haka ne kuwa, babu shakka yanda jama’a suka dauki yan Film ma abun ya zarce hakan saboda, yanzu iskan cin su na musamman ne suke tabkawa, ba sau daya ba ko sau biyu ba ire-iren wadan nan shaidoji suna fitowa daga bakunan jaruman.

Koda a kwanakin baya Tanimu Akawu fitaccen jarumin nan ya zargi ita kanta jarumar hadiza gabon, a wata hira da akayi dashi, inda yace, “Akasarin jaruman suna bin maza, yan siyasa da masu hannu dashuni, inda ya buga misali da jarumar Hadiza Gabon inda yace kalli, motar da Hadiza gabon take hawa, zata iya ninka tawa sau goma, Shin nawa ne ake biya a Film din duka? Inji dan cikin su Tanimu Akawu. Sannan Ya kara da cewa, kusan shekara 20 muke harkar nan, tun wadan nan ya mata basu fara Fitar DA nonuwa ba, muke harkar nan, amma su suna shigowa shekara daya biyu, sai kayi mamaki ina suke samun kudin su, yace ku duba Maryam Yahya, yaushe ta shigo harkar? Amma yanzu gata a cikin daula.

Wannan kenan.

Yanzu bari mu koma akan wadan Video na cin zarafi da akayi ma Amal, domin wancan Producer yace min, “Gabon ce ta biya kudi aka dauki yarinyar aka kawo mata ita har kaduna ta wulakantata, kuma ta tursasa mata fadin abunda ta fada.

Zancen gaskiya idan ka kalli wancan Video da wannan razanar da yarinyar akayi wajen janye zancen ta, amma babu shakka maganar hakan take gaskiya ne babu batun karya a ciki.

Domin sata akayi koda kake kallon Video zakaga yarinya amal a razane take, take bada hakuri bawai a nutse take ba.

Matan film a ma’aunin adalci.

Zancen gaskiya rankatakaf yan matan Film nan lalatattu ne sunma fi yanda al’umma take zato ma.

Duk cikin su, babu Wanda zata ce maka baban ta ne ya dauke ta ya kawo ta wannan harka, kenan, idan ka lura harkar bata arziki bace, harka ce ta amore a fandarewa ubangiji DA kuma iyaye.

koda yake suma da kansu suke fadin yanda suke kwashe da iyayen su kafin daga baya, idan iyaye sunga babu yanda za’ayi sai abarsu suyi abunda sukaga dama, don haka babu wani saurin uzri da wani zai kawo akan yan Film ba lalatattu Bane, sai dai duk da haka bazamu ce babu ba, amma sai Wanda Allah yaji kansa, shima tsaka tsakiya ne, wannan ina magana ne akan matan film, kenan.

A sashin maza ma kusan haka ne, saidai nasu da dan sauki ganin cewa, “akwai wadan da sun dan San abunda sukeyi suna kiyaye wasu abubuwa da dama, Wanda zai taba musu mutuncin su.

Shin zamu tsine musu ne?

Tabbas tsinuwa ko la’anta ga yan Film bai dace ba kwata-kwata, addu’a yaka mata muyi musu, domin tsinuwar nan har mu sai ta shafa.

Bari in baka misalin yanda zata shafe mu.

A yau mun wayi gari ko kaso ko kaki, sai an kalli Dirama a gidan, ka idan ka hana a faifai zaka iya hanawa a waya ba, idan ko ka hana ta waya ai in kasan wata baka San wata ba, sai su tafi YouTube su kalli abunsu.

To yanzu me zamuyi?

Babu shakka addu’a zamuyi musu, Allah ya shirye su, zuwa hanya madai-dai ciya, ko babu komai idan munayi musu addu’a babu shakka insha Allah wasu abubuwa munana Allah zai kaddara zasuyi sauki, koma ya canja wadan da suka fisu dama dama ya shigo dasu, wadan can kuma suyi waje Road.

Ya Allah mun tuba ka gafarta mana kada ka kamamu da laifin wawayen cikin mu.

Ita kuma Amina Amal da Yar Gabon, Allah ya shirye su, su tuba daga iskancin da sukeyi, idan ya tabbata sunayi, amma zarge zarge masu karfi, wadan da banga abunda zai iya Koran suba sun tabbata babu shakka sun aikata ba dai-dai ba, kawai sai yanzu Allah ya tona musu asiri, sai yanzu abun boye ya fito fili. Allah yasa wanna ya zama sanadiyyar shiryuwar su. 🙏

Daga Muhammad Ismail Ali.

Leave a Reply