SABUWAR ‘DAMARAR DA KE GABAN SHUGABA MUHAMMADU BUHARI:-

0
177

Alhamdulillah! Mai girma Shugaban ‘kasa ya cika alkawari, ya rattaba hannu kan dokar da za ta ba wa gwamnati da kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu damar fara biyan albashi mafi ‘karanci naira dubu talatain (30,000).

Shikkenan ‘yan ‘kwadago kuma “kanwa ta kar tsami ‘kwarnafin ya kwanta”. Sauran ‘yan ‘kasar da ba sa aikin gwamnati ko na hukumomi masu zaman kansu, su kuma sai su cigaba da cin ‘kaya, Allah kuma ya cigaba da raya su kamar kowa.

Su kuwa ‘yan Kwadagon sai su sake ji da wata gwagwarmayar ta tabbatar da ganin cewar dokar ta fara aiki a zahiri a kowane fanni na ma’aikatu.

Kamar yadda na fada a baya cikin wani rubutuna da ya gabata, kuma akasarin jama’a su ka sani, (Talakan Nageriya) ya na cikin matsi da ‘kuncin rayuwa. Irin ‘kuncin da inda ace ba Shugaba Muhammadu Buhari ba ne Shugaban ‘kasa, bai zama lallai Talakan ‘kasarnan ya lamunci zama cikin wannan yanayi ba.

Amma saboda ‘kauna da kuma kyautata zato da ake yi masa ‘yan ‘kasa suke cigaba da hakuri da jure yanayin da su ke ciki bisa tsammanin gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari za ta sama musu saukin rayuwa a nan gaba.

Mai girma Shugaban ‘kasa, Baba Buhari, ya zame mana dole mu magoya bayanka mu isar da koken talakawa zuwa gareka, domin fatanmu a gwamnatinka talaka ya ji dadin da bai taba jin irinsa ba a gwamnatocin da su ka gabata. Saboda yarda da ya yi da kai dan shi ka ke yi.

Mai girma Shugaban ‘kasa, kamar yadda masana su ke fada, aka kuma ga tasirin hakan a gwamnatocin baya, ‘karin albashi a ‘kasa wani tsani ne da ke ‘kara haifar da hauhawar farashin kayan masarufi.

Wannan dalili ya sanya muke fatan gwamnatinka ta sake ‘daura sabuwar ‘damara domin yin duk mai iyuwa wajen dakile matsalar da talaka ya ke tsoro ta hauhawar farashin kayan masarufi a sanadiyyar wannan ‘kari na albashi.

Baba a yanzu ma talakawa da dama su na rayuwa ne hannu-baka-hannu-kwarya, hauhawar farashin kayan masarufi kuwa babu abin da zai ‘karawa talaka face ‘kunci da damuwa. Irin yanayin da talaka ba ya tsammani a gwamnatinka.

Baba mu na fatan za ka tunkari wannam al’amari domin yi wa tufkar hanci. Mu kuma za mu raka ka da addu’ar samun nasara.

-Garba Tela Hadejia
Juma’a, 19/4/2019.

Leave a Reply