Zargin Cin Zarafi: Amina Amal Ta Maka Hadiza Gabon A Kotu, Ta Na Neman Diyyar Naira Miliyan 50

0
453

Amal na neman diyyar naira miliyan hamsin daga Gabon a kan abin da ta kira gallazawa da tozartawa.

Karshen tika-tika, tik! Amina Mohammed (Amal) ta bi shawarar masu cewa ta nemi hakkin ta a kotu kan lallasa ta da Hadiza Gabon ta yi, ta maka ta Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.

Amal na neman diyyar naira miliyan hamsin daga Gabon a kan abin da ta kira gallazawa da tozartawa.

Idan kun tuna, wasu hotunan bidiyo guda biyu sun bulla kwanan nan inda aka nuno Gabon ta titsiye Amal, har ta na mangarar ta, saboda wai Amal din ta zarge ta da aikata madigo.

A bidiyon, an ga Amal na amsa laifin ta, ta na kuma ba Gabon hakuri.

Jama’a sun yi caa kan al’amarin, wasu na goyon bayan Gabon, wasu kuma na cewa abin da ta yi wa karamar jarumar bai dace.

Wasu lauyoyi 12 sun saki takarda mai yin kira ga Amal da ta ba su amincewar ta su nema mata hakki a kotu.

Jaridar Daily Trust ta ranar Alhamis din nan ta ruwaito cewa Amal, wadda ‘yar kasar Kamaru ce, ta sa kotu ta aika wa Gabon da sammaci inda ta zarge ta da musgunawa, cin zarafi da kuma tsinka ta a idon duniya da sauran nau’o’i na wulakantarwa.

A sammacin, Amal ta ce kwace mata waya da Gabon ta yi, ta rike har tsawon awa 24, ta je ta karance duk sirrikan ta da ke cikin wayar, hakan shiga hakkin ta ne kuma ya saba wa sashe na 34 da na 37 na kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999.

Amal ta bukaci kotun da ta umarci Gabon da ta yi abu hudu: 1. ta ba ta hakuri a rubuce, 2. ta wallafa wannan bada hakurin a manyan jaridu guda biyu masu watayawa a kowane lungu na kasar nan, 3. ta na so kotu ta hana Gabon ko wani wakilin ta ya kara cin zarafin ta, sannan 4. ta na so Gabon ta biya ta diyyar naira miliyan 50.

Ita dai wannan rigimar ta jaruman, ta faro ne daga lokacin da Gabon ta tsoma baki cikin surutan da aka yi kan wasu hotuna da Amal ta tura a shafin ta na Instagram, ita kuma Amal ta yi sabon sako a Instagram din inda ta kira wata da ‘yar madigo.

Lauyoyi 15 ne su ka rattaba hannu a takardar karar da Amal ta yi, wadda kamfanin lauyoyi na A.A. Umar (SAN) da ke unguwar Farm Centre, Kano, ya shigar a kotun.

Mujallar Fim ta lura da cewa a sammacin ba a nuna ranar da ake so jaruman su bayyana kotu ba.

Ta yiwu sai yanzu ne shugabannin Kannywood za su tsoma baki cikin rikicin domin su sasanta jaruman kamar yadda su ka yi a rigimar Ali Nuhu da Adam A. Zango.

Leave a Reply