Dalilan da yake sa matan aure zina da karuwanci

0
1698

INA MAFITA?

Abinda muka tattauna jiya akan dalilan da yake sa matan aure zina da karuwanci ya matukar bayar da ma’ana, mutane da dama sun yi jawabi gwargwadon fahimtarsu, na karu sosai Allah Ya sakawa kowa da alheri.

Wato ‘yan uwa musulmi na jima ina tattara bayanai akan karuwanci wanda zan rubuta Littafi ya shiga kasuwa Inshaa Allah, nayi nazari sosai ta hanyar tattaunawa da matan da aka kamasu ana lalata dasu a cikin mota da kuma tattaunawa da karuwai masu zaman kansu.

Kazanta da sabon Allah da ake tafkawa da matan aure da ‘yan mata a cikin mota masu bakin gilashi a bypass ya munana matuka, har yasa ina saka alamar tambaya (????) akan duk mutumin da na ganshi ya sakawa motarshi bakin gilashi wato tinted, saboda irin abinda idona ya gane min a zahiri, suna ganin cewa kama dakin hotel tonon asiri ne, gwanda su sakawa motar bakin gilashi su aikata danyen aikin a cikin motar yafi.

Zakaga mutum ba wani babban attajiri ba, ba babban ‘dan siyasa ba, ba wani babban basarake ba, ba babban jami’in gwamnati ba, ba wani babban malami sananne ba, shi ba kowa ba, kawai dai Allah Ya dan rufa masa asiri ya sayi mota, ko ‘yan siyasa sun bashi mota sai yaje a sa mishi tinted, kashi 99 cikin 100 na irin wadannan mutanen ba alheri suke aikatawa a cikin motar ba.

Idan kuna so ku tabbatar da wannan jawabin da nake yi ku tambayi jami’an tsaro da suke patrol da daddare, ko kuma ku fara fita yawon dare don neman ilmi abinda ‘yan sanda suke cewa local knowledge.

Abu mafi tashin hankali shine ace matar aure ce take aikata zina, akwai wanda ba talauci bane yake saka su aikata wannan danyen aiki, domin ana kama matan manyan mutane attajirai.

A nawa fahimtar abubuwan da yake jefa matan aure cikin aikata laifin zina sune kamar haka:

-Rashin samun gamsuwar jima’i a gurin mijinta
-Rashin tsoron Allah
-Bakin talauci
-Buri
-Kawance da mata karuwai
-Jahiltar addinin musulunci
-Rashin samun kulawar mijinta
-Idan mijinta ya kasance mazinaci ne
-Kafofin sada zumunta
-Rashin zartar da hukunci
-Cin hanci da rashawa da karban toshiyar baki.

Wadannan dalilai guda 11 da na zayyano kowanne yana bukatar rubutu na musamman, wanda insha Allahu zanyi amfani da wannan damar na dinga gabatar da rubutu a kai muna tattaunawa daki-daki, domin a samar da mafita, a wayar da kan juna, a kuma ilmantar da juna.

Allah Ya yafe mana, Ya tsaremu Ya tsare al’ummar musulmi gaba daya daga fitinar karshen zamani Amin.

Daga Datti Assalafiy

Leave a Reply