MAGANA TA GASKIYA ITA CE:-

0
184

Daga Garba Tela Hadejia

Duk Shugaban wata ‘karamar hukuma ko Kansilan da ya gaza a Nageriya ‘karkashin tutar jam’iyyar (APC) to ya kamata jam’iyyar ta yi duk mai iyuwa wajen ganin ta ‘baro da shi daga kan kujerar a zabi duk wanda ake da yakinin zai damu da damuwar al’umma a ‘dora.

Saboda abin takaici da ta’ajibin ya yi yawa haka. Shugabannin ‘kananan hukumomi da Kansaloli sun fi duk wani Shugaba ta fuskar Siyasa kusa da talakawa, amma a dalilin gazawarsu yau kowane talaka ba shi da abin zagin da ya wuce Shugaban ‘kasa Buhari.

Gazawarsu ta kai ta kawo Talakawa ba sa bambance aikin Shugaban ‘kasa da na Gwamna da na shugaban ‘karamar hukuma da na Kansila. Duk wata ‘kura in Talaka ya kwasa sai ya ‘dora kan Shugaban ‘kasa, saboda Shugabannin da ke kusa da shi babu abin da su ke assala masa.

Haka kawai al’umma sun zuba ido sun sangartar da Ciyamomi da Kansaloli ta hanyar ‘dorawa gwamnoni laifin wai ai su ne su ke danne su, wai shi ya sa ba sa iya komai.

To mu ‘kaddara ma Gwamnonin su na danne sun, amma dannewar da su ke musun ai ba ta kai ta hana su aiwatar da abubuwan da za su taimaki rayuwar talakawan da su ke Shugabanta ba.

Yau an wayi gari ba ma wai ta batun Shugaban ‘karamar Hukuma ko wai wani Kansila ya zo ya yi maka wani abin azo a gani ake ba. Ko irin ‘yar yasar kwatar nan ma ba sa iya yi. (kula da tsaftar muhalli).

Balle su iya kula da wasu ‘yan matsaloli ta fuskar Ilimi da na Lafiya da na ruwan sha da samar da tsare-tsaren da za su rage zaman banza da tallafawa marayuwa da mabukata a iya unguwanninsu daidai gwargwado ba.

Kai matsala fa komai ‘kankantarta in ta same ku a unguwa in ba ku da hadin-kan da za ku magance kayarku, kuma ba ku da wani mutum mai zuciyar damuwa da damuwar al’umma, to fa sai da matsalar nan ta girma ta kashe ku amma babu abin da za su iya yi muku.

Kai ko maganin jinyar Naira dubu biyar (5000) in ba ka da yadda za ka yi kuma babu mai yi maka, in dan ta Kansilan mazabarka ne sai dai ka mutu.

Yanzu abin da aka ‘dauki Shugaban ‘karamar Hukuma ko Kansila shi ne, kawai mutum ya samu dama ya je ya warware matsalolin rayuwarsa kadai. An manta da gundarin manufar yi wa al’umma hidima.

Dan haka, yanzu ana daf! Da gudanar da zaben Shugabannin ‘kananan hukumomi da Kansilili a wasu daga cikin Jihohin Nageriya, mu na bawa Gwamnoni da Shugabancin jam’iyyarmu ta (APC) da sauran masu ruwa da tsaki da su dubi girman Allah, in ma ta hanyar masalaha ko zaben cikin gida a fiddawa al’umma mutanen da za su zama alkhairi a gare su.

-Garba Tela Hadejia
Lahadi, 21/4/2019.

Leave a Reply