BABBAR MAGANA: NA SHAFE SHEKARU BIYU DA RABI INA KWANCIYA DA MATAR AURE..!

0
1018

Mai karatu ya fahimci cewa wannan labarin da zan bayar, labari ne na gaskiya. Kuma dalilin da yasa zan bayar da shi, saboda ina son mutane su fahimci yanayin duniya, da kuma halin da mutum kan iya samun kansa a rayuwa, yanayi bayan yanayi.

Haka kuma ina rokon duk wanda ya karanta shi, ya nemarwa wannan matar gafarar Allah.

A shekaru da yawa da suka shude, wani
saurayi, ya samu kansa a cikin wani yanayi na jeka nayi ka, ya kasance ba ya iya tabukawa kansa komai na amfani, in ba domin Allah Ya hada shi da wannan matar auren ba.

Hakika wannan matar babu abin da zai ce
mata face Allah Ya saka mata da alkhairi, Ya
yafe mata dukkan kura-kuranta, Ya kuma
sanya aljanna ta zamo makomarta. Domin nima nasan yana sonta kuma yana alfahari da ita, zai iya fadar hakan a gaban kowama, duk da cewa, shi kansa idan ya tuno da wadancan shekarun biyu da rabi da suka share suna kwanciya a shimfida daya, yakan zargi kansa da abubuwa da yawa, kuma ina fatan Allah Ya yafe masa.

Kunsan Hausawa ke cewa ‘’ka so mai son ka‘’ to hakikanin gaskiya, a duk duniya Allah bai hadashi da wadda ta nuna masa soyayya ba tamkarta. Domin tun a lokacin da ta fara aza idanuwanta a kansa, Allah mai girma Ya jefa mata tsananin soyayyarsa a rayuwa, har ya kasance ta dauki soyayyar duniya ta dora a kansa, ba ta da lokacin mijinta kamar yadda take da lokacinsa.

Duk wani muradinta da farin cikinta ya tare kacokal a kansa. Abin da zai baka tsoro ma shine, tun a ranar da ta fara ganinsa, zuciyarta ta kasa hakurewa da soyayyarsa, har sai da ta rungume shi a kirjinta, tana mai cike da shauki da dauki a kan wannan sabon masoyi da Allah Ya hadata da shi a rana tsaka.

Abin bai tsaya a nan ba, har sai da ta kwana shimfida daya tare dashi a wannan ranar. Kuma daga wancan lokacin, kusan kowace rana hakanne yaci gaba da faruwa.

Kusancinsa da ita fa ba zai misaltu ba don har sai da ya kasance bata iya rabo dashi ko da na tsawon wuni daya ne, kuma ita ce take yi masa dukkan wata larura ta rayuwa da dan Adam ke bukata, amma a cikin kudin mijinta.

Wannan dalilin ne yasa shima ya fara tantancewa da dukkanin irin abubuwan
alfarmar da take yi masa, har ya fara zamowa, baya son kusantar kowa face ita. kamshin jikinta kawai yakan wadatar dashi, kuma ya kwantar da hankalinsa. Har aka wayi gari, idan ta nisance shi, nan take yakan zubar da hawaye, kuma ba zai dawo hayyacinsa ba har sai ya ji ta kusa da shi.

Watakila mai karatu ya yi tambaya to shi mijinta yana ina?

To abin da ya kamata mai karatu ya sani shi
ne: Duk da yake cewa mijin nata yakan yi
tafiye-tafiye, amma a sane yake da duk abin
da ke faruwa a gidansa. Amma ba shi da ikon hana faruwar hakan, saboda haka bai yi yunkurin hakan ba. Kuma hakanne yasa aka zauna lafiya har zuwa yau.

To shi yaron me ya sa bai kauracewa matar ba?

Ba shi da ikon yin hakan ne, saboda tuni ta
saye zuciyarsa, kuma ta gama mallaketa.
Duk fa larurarsa ita ce mai kula da ita. Idan ya rasa kudi ita ce mai ba shi, ita ce ke kula da dukkan abincinsa da abin shansa. Tufafin sakawarsa, daukar nauyin wanke su da goge su! Bayan hakan, idan ba shi da lafiya, ba shi da wanda ke jinyarsa sai ita, duk da cewa, yana da ’yan uwa barkatai.

Wannan ne ma yasa, nake iya cewa, da za’a
dauki dukkan abokansa da ’yan uwansa a
dora a sikeli daya, ba zasu dauki kashi daya na goman soyayyar da yake mata ba.

Wannan matar ba kowa bace face mahaifiyarsa (matar mahaifinsa), Ita ce take
matukar so da kaunarsa, tun ranar da ta
haifeshi, kuma take ta kwanciya dashi a
shimfidarta don gudun kada wani abu ya same shi, kuma a hakan take ta dawainiya dashi har tsawon shekara biyu da rabi ba tare da ta kasa ba, har ta yaye shi.

Mahaifinsa shine mijinta, wanda duk wata
larura a cikin dukiyarsa take yi masa, kunga ai ba zai hana a yiwa dansa larura ba!

Abin da nake nufi da abin da idan ya tuno
yakan yi nadama, shi ne: Duk da irin wannan
dawainiyar, wasu lokuta yakan sa6a musu
saboda ajizanci na dan Adam.

Haka abin yake a wurina, kamar kuma yadda yake a wurin kowa. Mahaifiya ba wasa ba fa!
Muyi la’akari da wannan dawainiyar kawai ta
shekara biyu da rabi, har yaushe zamu iya
biyan mahaifanmu ladar wannan gwarzon aiki.

Hakika mahaifa (musamman mahaifiya) sun
cancanci kowane irin nau’i na biyayya daga
wurinmu.

Ina fata Allah Ya albarkaci mahaifiyata da mahaifina da mahaifan masu wannan karatu a kan dawainiyar da suke yi damu. Allah Ya sa mu gama dasu lafiya. Wadanda suka rigamu gidan gaskiya kuwa, Ya Allah Ka jikansu da gafara.

Leave a Reply